Tun dama Tottenham na daya daga cikin kungiyoyin kwallon faka na Ingila mafiya girma amma ba ta taba cin lambar yabo a rukuni na daya ba tun daga 1961. Jose Mourinho ne madugu uban tafiyar kungiyar, kuma da alamar yana jagorantar kulob din da kyau.
Kungiyar Kwallon kafa ta Nice da ke wasa a gasar Ligue 1 ta kasar Faransa ta sallami kocinta Patrick Vieira.
Cristiano Ronaldo wanda dan asalin kasar Portugal ne ya zira kwallonsa ta 750 cikin shekarun da ya kwashe yana buga tamaula.
Kasancewa cikin gasar Premier League wani babban abu ne a wurin wasu kungiyoyin, kai wa ga maki 40 shi ne kawai babban burinsu. Yayin da kakar gasar ta fara gadan-gadan, wasu kungiyoyin za su fi damuwa ne da matakin da suke a gasar.
Masoyan Maradona sun zubar da hawaye tare da jefa firanni da rigunan kwallo a kusa da akwatin gawarshi yayin da a ka ajiye gawar a Casa Rosada a Buenos Aires na Argentina, ranar Alhamis.
‘Yan wasan Liverpool Mohamed Salah da Sadio Mane sun shiga jerin ‘yan wasa 11 da ke neani kambun zama zakaran duniya na FIFA a bangaren maza.
Tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya Daniel Amokachi ya bi sahun takwarorinsa a fagen wasan kwallo wajen nuna alhinin mutuwar shahararren dan wasa Diego Armando Maradona.
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ya mutu bayan fama da matsalar bugun zuciya, a cewar mai magana da yawunsa.
Ministan matasa da wasanni a Najeriya, Sunday Dare, ya fada a karshen mako cewa gwamnatin tarayya zata sake gyara tawagar kwallon kafa ta Supe Eagles domin ta taka rawar gani a fagen kwallon kafa na duniya.
Hukumar kwallon kafa ta duniya ta FIFA ta dakatar da shugaban hukumar CAF mai kula da harkokin kwallon kafa a nahiyar Afrika kuma mataimakin shugaban FIFA, Ahmad Ahmad, daga gudanar da harkokin wasannin kwallon kafa tsawon shekaru biyar.
Domin Kari