Kotun da ke yanke hukunci kan harkokin wasanni za ta yanke wani hukunci a yau Alhamis, kan ko a kara jaddada haramcin da aka sakawa ‘yan wasan tsalle-tsalle da guje-gujen Rasha, na shiga wasannin kasa da kasa dangane da zargin su da yin amfani da miyagun kwayoyi masu kara kuzari da hukumomin kasar suke marawa baya.
Hukumar yaki da shan kwayoyi masu kara kuzari ta duniya ta fitar da haramcin na shekara 4 a bara, inda ta hana ‘yan Rasha shiga wasanni da za’a yi masu zuwa na guje-guje da tsalle-tsalle a Tokyo, wasannin Olympic na shekarar 2022 da za a yi a China, da gasar kwallon kafa ta duniya ta 2022 da kuma sauran wasanni.
Rasha ta yi watsi da haramcin, tana mai kiran matakin a matsayin bi-ta-da-kullin-siyasa.
Ita dai Kotun da ke yanke hukunci kan harkokin wasanni ita ce mafi girma a fagen wasanni, kuma ta fada ranar Laraba cewa masu sasanta rikincin sun hadu da bangarorin biyu na tsawon kwanaki 4 a watan da ya gabata.