A sauran wasannin da aka yi a gasar ta Nations League, Italiya ta doke Isra’ila da ci 2-1, Erling Haaland ya taimakawa Norway doke Austria da ci 2-1
A ranar Lahadi aka kammala gasar ta Paralympics inda aka yi wasanni wuta a bikin rufe gasar.
Ita dai kasuwar cefanen ‘yan wasa ta Turkiyya tana bude har zuwa 13 ga watan Satumba.
A halin yanzu sai a watan Janairu za a sake bude kasuwar cinikayyar 'yan wasan.
A ranar Alhamis hukumar ta FIBA ta fitar da jerin sunayen kasashen.
Kafofin yada labaran Italiya sun ce Lukaku ya saka hannu kan kwantiragin shekaru uku a kungiyar ta Napoli wacce ke taka leda a gasar Seria A.
Fitar da sunayen ‘yan wasan na zuwa ne kwana guda bayan da aka nada Bruno Labbadio a mstayin sabon kocin kungiyar ta Super Eagles.
Hukumar ta NFF ta sanar cewa ta cimma matsaya da Labbadia dan asalin kasar Jamus, wanda shi ne koci na 37 da zai horar da ‘yan wasan na Najeriya.
Wannan shi ne wasa na farko da Madrid mai rike da kofin na La Liga ta samu nasara a wannan sabuwar kakar wasa.
Ita dai Argentina ita take rike da kofin duniya wanda ta lashe a Qatar a shekarar 2022.
Ma’aikatar za ta kaddamar da cikakken bincike kan dalilin da ya sa Najeriya ba ta tabuka komai ba a wasannin Olympics da aka kammala a Paris, in ji John Enoh.
Domin Kari