Najeriya ta fitar da tawagar ‘yan wasan da za su kara a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi badi.
Shafin kungiyarta Super Eagles ne ya fitar da sunayen ‘yan wasa 23 a ranar Laraba.
Najeriya za ta kara da Benin a ranar 7 ga watan Satumba a birnin Uyo, sai kuma a ranar 10 ga watan Satumba ta dangana zuwa Kigali domin karawa da Rwanda.
Fitar da sunayen ‘yan wasan na zuwa ne kwana guda bayan da aka nada Bruno Labbadio a matsayin sabon kocin kungiyar ta Super Eagles.
Wadannan wasanni za su zamanto zakaran gwajin dafi ga Labbadia wanda ya maye gurbin Finidi George.
Najeriya ce ta zo ta biyu a gasar AFCON da ta shude yayin da Ivory Coast da ta karbi bakuncin gasar ta lashe kofin bayan ta ci Najeriya ci 2-1.
Sau uku Najeriya na lashe kofin gasar ta AFCON, lokaci na na karshe shi ne a shekarar 2013 a Afirka ta Kudu.
Ta kuma lashe kofin a shekarar 1994 a Tunisia sai kuma a shekarar 1980 inda ta karbi bakuncin gasar.
Ga jerin ‘yan wasan dna Super Eagles:
Masu tsaron raga: Stanley Nwabali, Maduka Okoye, Amas Obasogie.
Masu tsaron gida: William Troost-Ekong, Bright Osayi-Samuel, Olisa Ndah, Bruno Onyemaechi, Oluwasemilogo Ajayi, Calvin Bassey, Olaoluwa Aina.
‘Yan wasan tsakiya: Wilfred Ndidi, Raphael Onyedika, Alhassan Yusuf Abdullahi, Fisayo Dele-Bashiru, Frank Onyeka, Alex Iwobi.
‘Yan wasan gaba: Samuel Chukwueze, Victor Osimhen, Kelechi Iheanacho, Victor Boniface, Moses Simon, Ademola Lookman, Taiwo Awoniyi.
Dandalin Mu Tattauna