Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Endrick Ya Kafa Tarihi A Real Madrid

Endrick
Endrick

Wannan shi ne wasa na farko da Madrid mai rike da kofin na La Liga ta samu nasara a wannan sabuwar kakar wasa.

Sabon dan wasan Real Madrid Endrick ya zama dan wasan Real Madrid na farko daga wata kasa kuma mafi karancin shekaru da ya kafa tarihin zura kwallo.

Endrick mai shekaru 18 ya canji Kylian Mbappe ne a karawar da Madrid ta yi da Valladolid a gasar La Liga a ranar Lahadi inda aka lallasa Valladolid da ci 3-0.

Wannan shi ne wasa na farko da Madrid mai rike da kofin na La Liga ta samu nasara a wannan sabuwar kakar wasa.

Mbappe ya ci wa kungiyar kwallo a wasan UEFA Super Cup inda suka kara da Atalanta a gabanin shiga sabuwar kakar wasa.

Sai dai har yanzu bai ci wa kungiyar kwallo ba a wasannin biyu da ta buga a bayan nan.

A wasan na ranar Lahadi dan wasan na Faransa ya fara bugawa kungiyar wasa a filin kungiyar na Santiago Bernabeu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG