Fitacce dan wasan kwallon golf din Amurka Tiger Woods ya yi wani mummunan hatsari a cewar ofishin ‘yan sandan birnin Los Angeles.
Cristiano Ronaldo ya kara haurawa da Juventus saman teburin cin kofin gasar 'Seria A' ta Italiya bayan da ya zuba kwallaye biyu duka da ka a karawarsu da Crotone.
Karawar hamayya ta cikin gida da aka yi ta ba Inter Milan damar wanke AC Milan da ci 3-0 lamarin da ya sa ta samu nasarar kara fadada tazarar da ke tsakaninsu.
Bayan da ta buga wasa 68 ba tare da an kada ita ba, Liverppol ta sha kaye a wasa hudu na baya-bayan nan da ta buga a gasar Premier League.
Dan wasan gaba na kungiyar Crystal Palace Wilfried Zaha ya ce zai daina gurfanawa a gwiwarsa kamar yadda ake yi kafin buga kowace wasan gasar Premier, domin karfafa fafutukar “Rayuwar Bakar Fata na da Muhimmanci.”
Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta Ingila ta nisanta kan ta da rahotannin da ake bazawa, da ke ta’allaka ta da zawarcin shahararren dan wasan Barcelona ta kasar Spain, Lionel Messi.
Tsohon dan wasan Chelsea Diego Costa na shirin kulla yarjejeniyar shekara biyu da kungiyar kwallon kafa ta Palmeiras da ke Brazil, wacce ya kasance yana kauna tun yana yaro.
Kungiyar kwallon kafa ta Burnley a gasar Premier ta Ingila, ta bi Crystal Palace har gida ta lallasa ta da ci 3-0.
Dan wasan Manchester United wanda har ila yau yake bugawa kasar Ingila kwallo, Marcus Rashford, ya ce magance matsalar cin zarafi a kafafen sada zumunta “abu ne mai sauki.”
Kungiyar Tampa Bay Buccaneers a Amurka, ta lashe kofin gasar NFL a wasan karshe na Super Bowl a Amurka.
Manchester City ta je har Anfield ta lallasa Liverpool da ci 1-4 a gasar cin kofin Premier ta Ingila.
Wasa tsakanin Liverpool da Manchester City a gasar cin kofin Premier, ba wasa ne da ke daukan hankalin masoya kwallon kafa a kasar ta Ingila kadai ba, har ma da sauran sassan duniya yayin da kowa ya zira ido ya ga yadda wannan wasa zai karkare.
Domin Kari