Saboda annobar coronavirus, ‘yan kwallo 25,000 kacal za a bari su shiga kallon wasan kwallon kafar Amurka na karshe da ake kira Super Bowl wanda za a yi a ranar Lahadi.
Wani rahoto da aka wallafa, ya nuna cewa kwantiragin Lionel Messi a Barcelona na tsawon shekara hudu ya kai euro miliyan 555.2 ko dala miliyan 673.8.
Manchester City ta zama club ta tara da ta zauna a saman teburin gasar Premier a wannan kakar wasa.
Kwanan nan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke wasa a gasar Premier ta Ingila ta sanar da Thomas Tuchel a matsayin sabon kocin club din.
Novak Djokovic da Rafael Nadal na shirin fara karawa a kakar wasa ta 2021 a gasar ATP ta Australian Open.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta sallami mai horar da ‘yan wasanta Frank Lampard daga mukaminsa bayan da kungiyar ta tsaya a matsayi na tara a teburin gasar Premier League ta Ingila.
Manchester United ta ci gaba da mallake saman teburin gasar Premier League bayan da ta tashi canjaras da tsohuwar abokiyar hamayyarta Liverpool a filin wasa na Anfield.
Kungiyoyin Manchester United da Liverpool na shirin gwada kaiminsu a ranar Lahadi a ci gaba da gasar Premier League ta Ingila.
Dan wasan Brazil Neymar da ke taka kwallo a kungiyar PSG ta kasar Faransa, yana kan tattaunawa da hukumomin kungiyar don ganin yadda zai tsawaita zamansa a kungiyar.
Manchester United ta zauna daram a saman teburin gasar Premier League ta Ingila bayan da ta doke Burnley da ci 1- 0.
Kungiyar Liverpool da take kan gaba a wasannin Firimiya Lig, ta sha kashi a hannun Southampton a jiya Litinin.
Dan wasan gaba na Black Stars, Jordan Ayew ya yaba wasan da kungiyarsa ta Crystal Palace ta yi a wannan sabuwar shekara, inda ta lallasa Sheffield United a wasan Firimiya Lig.
Domin Kari