Yanzu City ta ba Liverpool ratar maki 10 a teburin gasar yayin da ta ci gaba da zama a saman tebur a matsayin jagora.
Wannan nasara har ila yau ta ba City damar samun nasarar wasannin 14 a jere kenan a gasa daban-daban a kasar ta Ingila.
Dan wasan City Gundogan ne ya zira kwallo biyu, daya a minti na 49 daya kuma a minti na 73.
Amma kafin Gundogan ya zira kwallonsa ta biyu Mohamed Salah ya ramawa Liverpool kwallo daya da bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida.
Sai dai ba da jimawa ba, Sterling ya sake zira wata kwallon a ragar Liverpool a minti na 76 wacce ita ke rike da kofin gasar ta Premier.
Minti bakwai bayan kwallon Sterling, shi ma Foden ya durma wata kwallon a ragar ta Liverpool, lamarin da ya kai wasan zuwa ci 1-4.
Yanzu City na da maki 50, Manchester United na biye da maki 45, Leicester City na da maki 43 a matsayi na uku.
Liverpool na matsayi na hudu da maki 40 yayin da West Ham ke matsayi na biyar da maki 39.