“Na zaku na buga wasa tare da shi, ban san mai zai faru ba, amma ina matukar burin na ga ya zauna.” In ji Casemiro kamar yadda AP ya ruwaito.
Yau shirin na mu na cike da labaran wasanni masu kayatarwa: Kama daga batun dakatar da wasu 'yan wasu, zuwa batun cafanar da wasu da kuma shari'ar da wasu ke yi a kato da dai sauransu. Kar ka bari a ba ka labari.
Yayin da Manchester ke cafanar da Ronado zuwa wani kulub din Spain, su kuwa dubban magoya bayan Chelsea kira su ke a hana Anthony Tailor alkalancin duk wani wasan da Chesea ke ciki. Shi kuwa Amaju Pinnick na NFF ya ce ba shi ba tazarce.
Kocin Senegal Aliou Cisse ya ce wasan kwallon kafa na kasa-da-kasa - da kuma musamman gasar cin kofin kasashen Afirka – ba zai yiwu ya wasa mai martaba na biyu ba ga wasanni kulob kulob a Turai, ya kuma kalubalanci Napoli da ta ce kada a kara sayin ‘yan wasan Afirka.
Magana zarar bunu: Baki ba linzami ya jawo ma De Laurentiis rigima da CAF. Shi kuwa Ronaldo, har yanzu ribibinsa ake yi.
Yau za mu fi karkata ne ga gwabzawar da ake kan yi a Ingila a Wasannin Kasashe Rainon Ingila (CGames)
Kafin kotun ta yanke hukunci, tauraruwar kwallon kwandon ta Amurka Brittney Griner ta nemi afuwar 'yan uwanta da tawagarta yayin da ta saurari shari'ar da ake yi mata ta mallakar miyagun kwayoyi.
Domin Kari