Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zan So Ronaldo Ya Ci Gaba Da Zama A United – Casemiro


(Tsohon hoto) Ronaldo, dama tare da Casemiro, hagu a lokacin suna Real Madrid
(Tsohon hoto) Ronaldo, dama tare da Casemiro, hagu a lokacin suna Real Madrid

“Na zaku na buga wasa tare da shi, ban san mai zai faru ba, amma ina matukar burin na ga ya zauna.” In ji Casemiro kamar yadda AP ya ruwaito.

Sabon dan wasan Manchester United Casemiro, ya nuna sha’awar ganin Cristiano Ronaldo ya ci gaba da zama a kungiyar.

‘Yan wasan biyu wadanda abokanai ne, sun taka leda a kungiyar Real Madrid a gasar La Liga a shekarun baya.

A ranar Litinin Casemiro ya fadawa manema labarai hakan yayin da yake ban-kwana da kungiyar Real Madrid.

“Na zaku na buga wasa tare da shi, ban san mai zai faru ba, amma ina matukar burin na ga ya zauna.” In ji Casemiro kamar yadda AP ya ruwaito.

An ta yin yamadidin cewa Ronaldo zai bar Old Trafford idan aka bude kasuwar cinikin ‘yan wasa.

Hakan kuma na faruwa ne kakar wasa daya tak bayan da ya yi kome zuwa United daga Juventus a bara.

Magoya bayan United da dama na ganin zuwan Casemiro na da matukar muhimmanci duba da yadda tagomashin kungiyar yake ci gaba da dushewa, inda ta sha kaye a wasanninta biyu na farko a gasar Premier ta bana.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG