Ga dukkan alamu kasar Qatar ta shirya tsaf don karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.
Tawagar Portugal za ta kara da Najeriya a ranar Alhamis a wasan sada zumunta a Lisbon, daga bisani kuma sai ta nausa zuwa Qatar inda za ta fafata a gasar cin kofin duniya.
Hakan na nufin ya zama dole Ghana ta dauki Lawrence Ati-Zigi wanda shi ne zabinta na uku a matsayin mai tsaron raga.
Hukumar da ke yaki da tu’ammali da kwayoyin masu saka kuzari ta nemi a yanke masa hukuncin da ya fi wata 18.
Kasar Kamaru ta kimtsa tsaf ta shiga gasar cin kofin duniya karo na takwas a wannan shekarar bayan ta gaza halartar gasar ta baya da aka yi a kasar Rasha shekaru hudu da suka gabata.
Bayern ba ta yi karin haske kan girmar raunin na Mane ba, sai dai ta ce ba zai buga wasanta da Schalke a ranar Asabar ba.
Yayin da ake saura kwanaki 11 a fara gasar cin kopin duniya a Qatar, Senegal ta ce ba zata yi garajen yanke hukunci a kan dan wasanta Sadio Mane da ya samu rauni yayin wasan kungiyarsa ta Bayern Munich a wasan lig din kasar Jamus a jiya Talata cewa ba zai iya yin wasa a gasar cin kopin duniya ba.
An tsara jadawalin fafatawa a zagaye na 2 na gasar kwallon kafar cin kofin zakarun nahiyar turai, bayan kammala zagayen rukuni-rukuni.
Neymar ne zai jagoranci ‘yan wasan gaban, wadanda suka hada har da Vinicius Jr., Gabriel Martinelli da kuma Rodrygo.
Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Carlo Ancelotti dai ba zai dogara da Karim Benzema da Antonio Rudiger ba, saboda ba su kammala murmurewa daga raunukansu ba.
Dan wasan bayan Sipaniya da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Gerard Pique ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafar kwararru.
Domin Kari