Mai horar da ‘yan wasan kasar Brazil Tite, ya ce da ‘yan wasan gaba tara zai je gasar cin kofin duniya da za a fara a Qatar a wannan wata.
‘Yan wasan gaba suke da alhakin neman kwallo da kai hare-hare gidan abokan hamayya, kuma hakan da Brazil ta yi, manuniya ce cewa ta kimtsawa gasar.
Neymar ne zai jagoranci ‘yan wasan gaban, wadanda suka hada har da Vinicius Jr., Gabriel Martinelli da kuma Rodrygo.
Daga kuma jerin ‘yan wasan kasar 26 da za su wakilci Brazil a Qatar, har da Dani Alves mai shekaru 39.
Mai horar da ‘yan wasan Tite ya ce curo ‘yan wasan ne daga jerin ‘yan wasa 55 da suka yi ta bibiyarsu tun daga 2018.
Brazil na rukunin G tare da Serbia, Switzerland da kuma Kamaru.