Za a sake wani gwajin na biyu domin tabbatar da na farko, idan kuma har aka samu Pogba da laifi, zai iya fuskantar hukuncin haramcin buga wasa na tsawon shekara hudu.
Rubiales ya kuma sanar da ajiye aikinsa na hukumar UEFA inda yake rike da mukamin mataimakin shugaban hukumar.
Rubiales ya shiga matsala bayan da ya sumbaci wata 'yar wasan kasar ta Sifaniya a labbanta ba tare da izininta ba a lokacin da ake bikin ba da kyautukan lashe kofin gasar mata ta duniya da kasar ta yi.
A ranar Juma’a gasar ta Premier ta bana za ta kankama, inda City za ta kai wa Burnley ziyara a gidanta a wasan farko.
Ingila ta doke Najeriya da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida a yau Litinin, inda ta samu nasarar tsallakewa zuwa matakin daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin kwallon kafa ta mata ta FIFA, wadda Australia da New Zealand ne masu masaukin baki.
Yanzu Sweden ta kai zagayen quarter-final inda za ta kara da Japan wacce ta doke Norway da ci 3-1 a jiya Asabar.
A ranar Asabar za a bude zagayen da karawa tsakanin Switzerland da Spain, sai karawa ta biyu tsakanin Japan da Norway.
Ita dai Ingila ta lashe wasannin uku a jere ba tare da ta shan kaye ba, yayin da ita kuma Najeriya ta yi canjaras sau biyu ta kuma shammaci Australia da ci 3-2.
Kungiyar Super Falcons wacce ita ce ta 40 a iya taka leda a fagen wasan kwallon kafa na mata a duniya, ba ta sha kaye ko daya ba a wasannin da ta buga, yanzu kuma ta doshi zagayen kwaf-daya.
Shi dai Obi a birnin Jos ya girma, kuma ya fara wasan kwallonsa ne a garin inda daga baya ya shahara.
Shugaba Ahmed Bola Tinubu ya mika sakon fatan alheri ga 'yan wasan kwallon Najeriya na Super Falcons yayin da suke shirye-shiryen karawa da Australia a wasansu na biyu na rukuni a gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA da ke gudana a Australia da New Zealand 2023.
Kasar Netherlands ta fara wasan rukunin E da yin nasara da ci 1-0 a kan kasar Portugal a gasar cin kofin duniya ta mata da aka buga a filin wasa na Dunedin a yau Lahadi, kuma Stefanie Van der Gragt ce ta ci kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci na wasan bayan bitar na’urar VAR.
Domin Kari