Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Cin Kofin Duniya Ta Mata: Sweden Ta Fitar Da Amurka Mai Rike Da Kofi


'Yan wasan Sweden suna murnar fitar da Amurka a bugun fenariti 5-4
'Yan wasan Sweden suna murnar fitar da Amurka a bugun fenariti 5-4

Yanzu Sweden ta kai zagayen quarter-final inda za ta kara da Japan wacce ta doke Norway da ci 3-1 a jiya Asabar.

Sweden ta fitar da Amurka a gasar cin kofin duniya ta mata a bugun fenariti da ci 5-4, bayan da har aka yi karin lokaci ba tare da wani bangare ya zura kwallo ba.

‘Yar wasan Sweden Lina Hurtgis ce ta buga fenariti ta karshe wacce mai tsaron ragar Amurka Alyssa Naeher take takaddama kan cewa ba ta shiga raga ba, amma aka gano cewa kwallon ta riga ta tsallaka layin ragar.

Ita dai Amurka sau hudu tana lashe kofin, kuma ita take rike da kofin a halin yanzu, yayin da ta yi yunkurin kafa tarihin lashe kofin a karo na uku a jere.

Yanzu Sweden ta kai zagayen quarter-final inda za ta kara da Japan wacce ta doke Norway da ci 3-1 a ranar Asabar.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG