An sanar da tawagar kasar Jamus da zata wakilci kasar a gasar Euro 2024, tare da dan wasan tsakiya na Bayern Munich Aleksandar Pavlovic, da dan wasan gaba na Hoffenheim Maximilian Beier da kuma dan wasan Stuttgart Chris Führich wandanda basu taba shiga wannan gasa ba lamarin da ya zo da al’ajabi.
Ana dai ta hasashen Mbappe zai nufi gasar La Liga ne inda zai bugawa Real Madrid a kakar wasa mai zuwa.
Shekara bakwai Mbappe ya kwashe yana bugawa PSG wasa, inda ya zura kwallaye 255 amma bai kai ga lashe kofin zakarun turai ba.
Alkalin wasa Jarred Gillett zai daura kyamara a goshinsa a yayin fafatawar gasar firimiya da za’a yi a yau Litinin tsakanin Crystal Palace da Manchester United, a cewar hukumomin shirya gasar.
Nasarar na zuwa ne bayan da ‘yan wasan Carlo Ancelotti suka lallasa Cadiz da ci 3-0 a ranar Asabar yayin da Barcelona ta sha kaye a hannun Girona da ci 4-2.
A makon da ya gabata Salah da Klopp suka yi musayar kalamai a gaban jama'a a wasan da Liverpool ta buga da West Ham wanda aka tashi da ci 2-2.
Ba a san dai mai ya janyo fadan ba, amma dukkan alamu sun nuna cewa kowa cikin bacin rai yake magana a hotunan bidiyon da aka nuna wasan na Liverpool da West Ham.
Ita dai Leicester wacce ke taka leda yanzu a mataki na biyu na Premier ta kasance a gaba a teburin gasar.
Wannan ne karo na 3 da zakarun kasar Ugandan suka yi rashin nasara a matakin rukuni inda suke da kwantan wasa 3. Saidai mai tsaron bayan Oilers, Robinson Opong ya dage akan cewar ba zasu mika kai ba.
Wani zakaran dara na wasan Chess, ‘dan Najeriya kuma mai fafutukar koyar da ilimin yara yana kokarin buga dara na tsawon sa'o'i 58 ba tare da tsayawa ba a dandalin Times Square na birnin New York domin karya tarihin duniya na tsawon wasan chess mafi dadewa.
Rabon da tawagar mata ta Najeriya ta je gasar tun shekaru 16 da suka gabata.
OJ Simpson ya kasance 76
Domin Kari
No media source currently available
1. Messi ne mafi cin kwallo a Argentina, kuma mafi taimakawa a ci kwallo 2. Babu wani a La Liga da ya taba cin kwallo da bugun ‘freekick’ fiye da Messi 3. A La Liga, Messi ne ya fi cin kwallo sau uku a wasa guda. 4. Babu shahararren dan wasan kwallon kafa da aka yi ta sa hotunansa a kwalayen...
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ya mutu bayan fama da matsalar bugun zuciya, a cewar mai magana da yawunsa.
Ga zabin VOA na jerin gwarzayen ‘yan wasan kwallon kafar Afirka biyar da za su buga wasa a yau. Wasu daga cikinsu sanannu ne – yayin da ta yi wu, ba ku san wasunsu ba…. tukuna. Su waye a jerin fitattun ‘yan wasanku a fagen kwallon kafar nahiyar Afirka a yau?