Tayoyin mota da aka jefar ka iya zama shara ko kuma kayan amfani. A Senegal, wasu dalibai sun kafa kamfani da ke sarrafa tsofaffin su zama abubuwan amfani.
PSG ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin tana mai cewa dan wasan mai shekaru 29 ya kuma yage jijiyoyin sawun sa. Shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin raunin da ya faru.
Dan wasan PSG, Lionel Messi, ya ci kofin Ballon d’Or na shekarar 2021 bayan da yayi bajinta ta ba saban ba a wannan shekarar.
Kungiyar Paris Saint-German ta ce Neymar zai kaurace ma wasa na tsawon mako takwas saboda raunin da ya ji a idon kafa.
A daren Litinin ne ake bikin karama gwarzayen shekara a haujin kwallon kafar duniya da aka fi sani da Ballon d’Or, a birnin Paris na kasar Faransa.
Ko dai Italiya ko Portugal na da tabbacin ba za su buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a shekara mai zuwa ba, bayan da aka hada su a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da aka yi ranar Juma'a a zagaye na biyu na neman shiga gasar Turai.
Liverpool ta sake yin wani gwaninta wajen kai hari inda ta lallasa Southampton da ci 4-0 wanda hakan ya sa kungiyar ta tsallake zuwa mataki na daya a teburin gasar Premier ta Ingila. Kungiyar ta Reds sun ci akalla kwallaye biyu a wasanni 17 da suka yi a duk gasa.
Liverpool na fuskantar saurin juyewa a wasan Premier da Southampton.
Wasan Zabuwa, wasa ne na shekara-shekara na Zabarmawa da Adarawa, ‘yan asalin Nijar dake zaune a kasar ta Ghana.
Daruruwan magoya baya suka karrama fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ranar 25, ga watan Nuwamba 2021, da ya cika shekara guda da mutuwa.
Messi, Ronaldo, Mbappe, da Lewandowski suna cikin jerin sunayen ‘yan wasan da FIFA ta fitar da za ta ba kyautar gwarzon dan wasa na shekara.
Domin Kari
No media source currently available
1. Messi ne mafi cin kwallo a Argentina, kuma mafi taimakawa a ci kwallo 2. Babu wani a La Liga da ya taba cin kwallo da bugun ‘freekick’ fiye da Messi 3. A La Liga, Messi ne ya fi cin kwallo sau uku a wasa guda. 4. Babu shahararren dan wasan kwallon kafa da aka yi ta sa hotunansa a kwalayen...
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ya mutu bayan fama da matsalar bugun zuciya, a cewar mai magana da yawunsa.
Ga zabin VOA na jerin gwarzayen ‘yan wasan kwallon kafar Afirka biyar da za su buga wasa a yau. Wasu daga cikinsu sanannu ne – yayin da ta yi wu, ba ku san wasunsu ba…. tukuna. Su waye a jerin fitattun ‘yan wasanku a fagen kwallon kafar nahiyar Afirka a yau?