Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasanni a Takaice


Filin Wasan Manchester City
Filin Wasan Manchester City

A daren Litinin ne ake bikin karama gwarzayen shekara a haujin kwallon kafar duniya da aka fi sani da Ballon d’Or, a birnin Paris na kasar Faransa.

An dawo da bikin ne a wannan shekara ta 2021, bayan da aka dage na shekarar bara ta 2020, sakamakon annobar coronavirus.

Zaratan ‘yan kwallon 30 ne ke cikin jerin sunayen ‘yan takarar gwarzon shekara na bana, da suka hada har da dan kasar Argentina Lionel Messi da ke taka leda a kungiyar PSG, da ya lashe lambar a biki na karshe da aka gudanar a shekarar 2019.

Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta Ingila ta tabbatar da daukar tsohon kocin RB Leipzig, Ralf Rang-nick a zaman sabon mai horar da ‘yan wasan kungiyar na rikon kwarya, bayan sallamar Ole Gunnar Solskjaer.

Ronaldo da sauran 'yan wasan United bayan wasansu da City
Ronaldo da sauran 'yan wasan United bayan wasansu da City

Rang-nick dan kasar Jamus mai shekaru 63, zai baro kungiyar Lokomotiv Moscow ta kasar Rasha, inda ya ke a matsayin manajan bunkasa lamurran wasanni.

Da farko dai kocin bai da sha’awar karbar aikin na United saboda kasancewarsa na dan takitaccen lokaci na watanni 6 kacal, to amma kuma daga bisani ya amince da tayin bashi aikin ba da shawarwari na tsawon shekara 2 a United din, bayan kammala aikin sa na koci na rikon kwarya.

Hukumar kwallon kafar duniya – FIFA, ta nada wasu kwamitocin daidaita al’amura a kasashen Afirka 2, wato Chadi da Guinea.

FIFA
FIFA

Matakin ya biyo bayan rigingimu da ake fama da su a hukumomin kwallon kafar kasashen biyu, da har yanzu ba su da tabbatattun zababbun shugabanni.

Al’amarin kasar Chadi dai ya biyo ne bayan janye dakatarwa da kungiyar da akayi daga wasannin kwallon kafa na kasa-da-kasa, sakamakon katsalandan na gwamnatin kasar.

A kasar Guinea kuma an gudanar da zaben shugabannin hukumar kwallon kasar, to amma hukumar FIFA ta ce zaben na tattare da magudi da saba dokoki.

An dorawa kwamitocin alhakin daidaita al’amura a hukumomin kwallon kasashen 2, tare da gudanar da zabukan sabbin shugabannin hukumomin, inda na Chadi kuma aka kara masa da aikin ci gaba da tattaunawar da aka soma, ta sasantawa da daidaitawa tsakanin hukumar kwallon kafa da gwamnatin kasar.

A kasar Kenya kuma an ci gaba da tsare shugaban hukumar kwallon kafar kasar,, bayan da aka gurfanar da shi a gaban kotu, bisa tuhumar aikata laifuka 4 da suka shafi almundahanar kudade.

Nick Mwendwa
Nick Mwendwa

Hukumar binciken manyan laifuka ta kasar ce ta tuhumi Mwendwa da wasu mutane da laifin wawure kudi da adadinsu ya kai kimanin dalar Amurka 337,200.

Mwenda ya kasance tsare a gidan kaso tun ranar Juma’a, sa’adda aka sake kama shi karo na 2, bayan ba da belinsa a kamun da aka yi masa na farko, makwanni 2 da suka gabata.

Takardun shigar da kara na ‘yan sanda sun bayyana cewa ana tuhumar Mwenda da sauran wadanda ake zargin, sun aikata laifin ne tsakanin 4 ga watan Maris zuwa 31 ga watan Mayun wannan shekara.

A ranar Alhamis da ta gabata hukumar kwallon kafar kasar ta ba da sanarwar cewa an kai karshen tuhumar da ake masa, a yayin da kotu ta maida masa da kudinsa da ya biya na neman beli, to amma daga bisani ‘yan sanda suka ce wata karar ce dai, amma ba tuhumar almundahar kudaden ce aka rufe ba.

a/italiya-ko-portugal-ba-za-su-iya-shiga-gasar-cin-kofin-duniya-ta-2022-ba-bayan-da-aka-tashi-da-ja-a-gasar-turai

a/liverpool-ta-lasa-southampton-a-sabon-gasa

a/minene-makomar-manchester-united-bayan-korar-solskjaer

Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG