Paris Saint Germain ta ce tana bibiyar lamarin tare da shan alwashin daukan matakin da ya dace a karshe.
Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer? Saurari cikakken rahoton Murtala Faruk Sanyinna.
Sakamakon wannan wasa ya ba City damar matsawa zuwa matsayi na biyu a teburin gasar ta Premier.
Bayan nadin wani dan Jamhuriyar Nijar, kuma dan asalin Birni N'Konni a matsayin shugaban zabi sonka na nahiyar Afirka, ana ci gaba da gudanar da shagulgula a garin Birni N'Konni da suka hada da wasan damben gargajiya.
Kazalika kungiyar ta PSG ta bayyana cewa Marco Verratti, shi ma bai zai buga wasan ba, saboda yana kan murmurewa daga wata jinya.
Wasa tsere da kananan katakai masu tayoyi, wato Skateboarding, wasa ne da ya samu ci gaba, inda har ake yin shi yanzu a wasannin Olympics na lokacin bazara.
Masu lura da al’amura a fannin wasan kwallon kafa sun ce ajiye Pogba da aka yi a benci a wasan United da Liverpool bai yi masa dadi ba.
Haaland ya ci wa Dortmund kwallaye 70 a wasanni 69 tun bayan da ya koma kungiyar daga Red Bull Salzburg a shekarar 2019.
An sauya shi da Kai Havertz bayan da ya gurde kwaurinsa a lokacin da dan wasan Malmo Lasse Nielson ya kwade shi.
A birnin Jos na Najeriya, kungiyar masu tseren keke reshen jihar Filato ta shirya gasar tseren keke ga kananan kungiyoyi da mutane a birnin Jos, a wani yunkuri na bunkasa wasan tseren keke a jihar.
Ita dai Real ta ce a shirye take ta biya fam miliyan 197 don sayen dan wasan dan asalin kasar ta Faransa.
Akwai alamu da ke nuna cewa mai yiwuwa Rudiger ya ci gaba da zamansa a Stamford Bridge.
Domin Kari
No media source currently available
1. Messi ne mafi cin kwallo a Argentina, kuma mafi taimakawa a ci kwallo 2. Babu wani a La Liga da ya taba cin kwallo da bugun ‘freekick’ fiye da Messi 3. A La Liga, Messi ne ya fi cin kwallo sau uku a wasa guda. 4. Babu shahararren dan wasan kwallon kafa da aka yi ta sa hotunansa a kwalayen...
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ya mutu bayan fama da matsalar bugun zuciya, a cewar mai magana da yawunsa.
Ga zabin VOA na jerin gwarzayen ‘yan wasan kwallon kafar Afirka biyar da za su buga wasa a yau. Wasu daga cikinsu sanannu ne – yayin da ta yi wu, ba ku san wasunsu ba…. tukuna. Su waye a jerin fitattun ‘yan wasanku a fagen kwallon kafar nahiyar Afirka a yau?