Hotunan Izreal Zakari Galadima tare da Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima, wanda ya samu maki mafi girma a sakamakon jarabawar JAMB a shekarar 2018, da dalibai ke rubutawa kafin su samu su shiga jami'a
Hotunan gidajen da suka ruguje a wani kauye dake kewayen Yamai a Jamhuriyar Nijer sakamakon ambaliyar ruwa.
Shugaban hukumar zaben kasa INEC, Prof. Mahmood Yakubu ya gana da Kwamitin shugabani da daraktocin hukumomin zaben jihohin Najeriya NCC, kan yadda za'a fitar da sakamakon zabe bayan zabe ta hanyar amfani da na'urar kwamfuta.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya gudanar da taron manema labarai.
Sanata Bukola Saraki da kakakin Majalisar Dokoki sun yi wani taro da Hukumar jami'an zabe, INEC yau Laraba a birnin tarayya Abuja.
Dambarwar Siyasar Najeriya na daukar sabon salo, inda Jami'an tsaro suka garkame Kofofin shiga Majalisar dokokin Kasar duk da cewa ya'yan Majalisar suna hutu.Wannan ya hana kananan ma'aikata da ma yan jaridu shiga Majalisar domin daukan labarin wani taro da aka ce za a yi.
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbanjo ya halarci taron shirin bada lambar yabo ga masu kanana da matsakaitan sana'a MSME na shekarar 2018, a babban dakin taron 'yan Majalisu da ake cewa Confrence Center dake Abuja.
Maitaimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya karbi wakilan babban bankin duniya da suka kawo ziyara a fadar shugaban kasa.
A Jamhuriyar Nijer kungiyoyin nakasassu sun yi zaman dirshan a harabar ma'aikatar ministan jin dadin al'umma, Inda suka nuna rashin jin dadi akan abin da suka kira da tauye hakkokin nakassasu.
An farfado da aikin hanyoyin jirgin kasa da ya tashi daga jihar Warri zuwa jihar Kogi da aka shimfide shekaru 30 da suka gabata, ana sa ran kamala tashar jirgin kasar nan ba da dadewa ba, kuma ana shirin hanyar jirgin kasar zai issa har Arewacin Najeriya.
A yau ne 31 ga watan yulin 2018, Mataimakin Shugaban Kasa Prof Yemi Osinbajo, tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta kasa sun kaddamar da wani sabon shirin da zai baiwa mararsa lafiya dokar yanci, domin inganta harkar lafiya a kasar.
Domin Kari