An karama matar shugaban kasa Aisha Muhamadu Buhari da digirin girmamawa a jami'ar Asan dake Korea Ta Kudu.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbanjo ya kai ziyara sansanin tashar jirgen ruwa da ake sauke kaya da ake cewa LADOL free zone, inda ya zagaya ya duba kayayyakin aikin dake sansanin a .Apapa, jihar Lagos
Hotunan Izreal Zakari Galadima tare da Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima, wanda ya samu maki mafi girma a sakamakon jarabawar JAMB a shekarar 2018, da dalibai ke rubutawa kafin su samu su shiga jami'a
Hotunan gidajen da suka ruguje a wani kauye dake kewayen Yamai a Jamhuriyar Nijer sakamakon ambaliyar ruwa.
Shugaban hukumar zaben kasa INEC, Prof. Mahmood Yakubu ya gana da Kwamitin shugabani da daraktocin hukumomin zaben jihohin Najeriya NCC, kan yadda za'a fitar da sakamakon zabe bayan zabe ta hanyar amfani da na'urar kwamfuta.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya gudanar da taron manema labarai.
Sanata Bukola Saraki da kakakin Majalisar Dokoki sun yi wani taro da Hukumar jami'an zabe, INEC yau Laraba a birnin tarayya Abuja.
Dambarwar Siyasar Najeriya na daukar sabon salo, inda Jami'an tsaro suka garkame Kofofin shiga Majalisar dokokin Kasar duk da cewa ya'yan Majalisar suna hutu.Wannan ya hana kananan ma'aikata da ma yan jaridu shiga Majalisar domin daukan labarin wani taro da aka ce za a yi.
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbanjo ya halarci taron shirin bada lambar yabo ga masu kanana da matsakaitan sana'a MSME na shekarar 2018, a babban dakin taron 'yan Majalisu da ake cewa Confrence Center dake Abuja.
Maitaimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya karbi wakilan babban bankin duniya da suka kawo ziyara a fadar shugaban kasa.
Domin Kari