A cewar shugaban kasar, ana sa ran sabon kamfanin ya fara aiki kafin karshen zango na 2 na sabuwar shekarar, kuma hadin gwiwa ne tsakanin hukumomin gwamnatin da suka hada da BOI, NCCC, NSIA da ma'aikatar kudin kasar da bangaren kamfanoni masu zaman kansu da kuma kamfanonin kasa da kasa.