Sakamakon binciken da wata cibiya mai zaman kanta take gudanarwa mako mako a fannin kiwon lafiya na nuni da cewa, komanin mutane bakwai cikin goma na ‘yan Najeriya sun yi fama da zazzabin cizon sauro a shekarar da ta gabata.
Likitoci dake kula da mata sun yi gargadi da cewa, shan magani ba tare da izinin likita ba yana da hadarin gaske ga mata masu ciki.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, ana iya shawo kan zazzabin cizon sauro. Majalisar Dinkin Duniya tace zuba jari a kan yaki da zazzabin cizon sauro zai taimaka a yunkurin kula da lafiyar al’umma.
Masu bincike sun gano cewa akwai maganin da yake da kaifi da yafi amfani wajen jinyar yara dake da kananan yara dake dauke da kwayar cutar HIV sai dai maganin yana da tsadar gaske, kuma ba a samunshi sosai kasashe masu tasowa.
An kaddamar da wani sabon tsarin yakin cutar shan inna. Cibiyar yaki da cutar shan inna ce ta kaddamar da sabon kamfen na tsawon shekaru shidda a Abu Dhabi.
Wani sabon rahoto daga wata kungiyar agaji ta kasa da kasa ya ce, kwanakin jarirai na farko a duniya su ne mafiya kasada a kusan kowace kasa, a ciki har da Amurka.
Domin Kari