An inganta yadda ake bayarda maganin rigakafin Polio a Jihar Bauchi saboda yaran dake shigowa daga makwabtan jihohi inda cutar ta yi tsanani
Kwararru sun bayyana cewa, zubar jinni fiye da kima yana kashe mata lokacin haihuwa.
Kungiyar Likitocin Harhada Magunguna ta Najeriya ta ce rashin sanya 'ya'yanta cikin wannan aiki, yana rage masa kaifi da baza kwayar cutar
A jihohin arewacin Najeriya, wadanda cutar Polio ta nakkasa sune ke bi gida-gida domin shawo kan iyaye su kyale a ba ‘ya’yansu maganin rigakafi
Shugaban asibitin Maisamari dake garin Maradi Ibrahim Sabbi ya bayyana cewa rashin tsabta yana iya sa mutane su kamu da zazzabin cizon sauro wanda yafi kama kananan yara, kamar jarirai zuwa shekaru biyar.
FOMWAN a Jihar Borno tana fadakar da iyaye muhimmancin yi wa 'ya'yansu rigakafin kamuwa da cutar Polio, ko shan inna
Wani sabon bincike na masana a kasar turai, ya bayyana cewa likitoci sun sami nasara wajen samar da isashshen nono ga mata masu shayar da yara ta wurin yin amfani da wani ruwan magani da ake kira insulin.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, kashi saba'in cikin dari na masu fama da zazaabin cizon sauro suna nahiyar Africa.
Masana sun ce barin cikin mata ba abin da za a iya hanawa ba ne, musamman mata masu ciki da ba su kai wata uku ba
Sakataren Hukumar Kula da Lafiya tun daga matakin farko na babban birnin tarayya, Dr. Rilwanu Mohammed, yace za a hada kai da kungiyar NURTW don wannan aiki
Musamman kungiyar dake tallafawa wajen yaki da wannan cuta, ta nuna damuwa da yadda cutar ta yi katutu a Najeriya
Domin Kari