Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Rotary Ta Nemi Karin Hadin Kai Kan Polio


Kungiyar Rotary tana gudanar da aikin rigakafin cutar Polio a Kaduna, Najeriya (Rotary International)
Kungiyar Rotary tana gudanar da aikin rigakafin cutar Polio a Kaduna, Najeriya (Rotary International)

Musamman kungiyar dake tallafawa wajen yaki da wannan cuta, ta nuna damuwa da yadda cutar ta yi katutu a Najeriya

Shugabannin dake jagorancin yunkurin kawar da cutar Polio daga doron kasa, sun yi kiran da a kara hada kai a yunkurin kawar da wannan cuta mai nakkasawa da kuma kisa daga doron kasa. Su na wannan kiran ne a karshen babban taron kolin kungiyar Rotary International a Lisbon, a kasar Portugal.

Musamman ma dai, shugabannin sun bayyana damuwa kan yadda kwayar cutar Polio ta ke ci gaba da bulla a wasu kasashe guda uku, musamman Najeriya da Pakistan da kuma Afghanistan.

Shirin Yaki Da Cutar Polio a Duniya, ya kuduri aniyar ganin an kawo karshen wannan cuta nan da shekarar 2018. ‘Yan Riotary da suka halarci wannan taron koli sun bayar da tabbacin cewa ana iya cimma wannan gurin.

Dukkan wadanda suka yi jawabai sun bayyana cewar idan har ba a samu hadin kai a tsakanin gwamnatoci da kuma sassa masu zaman kansu ba, to zai yi wuya a iya kawar da wannan cuta.

Babban abinda ya fi damun mahalarta wannan taron shi ne dukkan sauran kasashen da suka rage da wannan cuta ta Polio yanzu a duniya, kasashe ne dake fama da rikice-rikicen siyasa, zub da jinni da kuma wasu al’adun da suke kawo cikas ga bayar da magungunan rigakafi ga yara da sauran wadanda suke bukatar kariya daga wannan cuta.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG