Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahimmancin Tsabtar Abinci a Kiwon Lafiyar Jama’a


Wata mata tana girki
Wata mata tana girki

Ilimin tsabtar abinci na nufin tsabtar da ake dauka wajen shirya abinci da kayan girki.

Ilimin tsabtar abinci na nufin tsabtar daake dauka wajen shirya abinci da kayan girki. Mutane da yawa suna danganta wannan da wankin hannuwa kamin cin abinci. Amma tsabtar abinci mai kyau ta wuce wannan. Rashin tsabtar abinci shine ke kawo dukan cututtukan da zamu iya kaudawa har da mutuwa.

Mahimmancin tsabtar da ta danganci abinci tana farawa da shirin abincin. Danyen kayan da akayi amfani dasu wajen dafa abincin dole a wanke su da kyau da ruwa. Dole kuma a maida hankali sosai ga abinda za’a ci danye, kamar su ganye ko kuma ‘ya’yan itace. Idan yayiwu, a wanke su da ruwan zafi. Wannan yana da amfani domin akwai matsalar bacin ganyayen, kuma domin kiyaye daukan kwayar cuta a ‘ya’yan itace da aka tauna daga kasa. Kwayoyin cuta da yawa kamar masu kawo cutar typod, zawo, ciwon kwankwaso, harda cutar hanta, da sauransu, suna samuwa cikin bayan garin wadanda suke fama da wadanan cututukar. Idan suka yi bayan gari a kasa, wannan kasar mara kyau zata iya zama mai yada cutar.

Ana bukatar dama mai yawa domin tsabtace kayan nama. Wanda aka yanka danye ko wanda ba’a dafa ba zai iya zama hanyar kamuwa da wata cuta mai zafi sosai. Wurin da aka yi amfani wajen yanka naman da kuma wukar ya kamata a tsabtace su. Idan yayiwu wanda ya rike naman yasa safar hannu wurin rike naman. Ya kamata a dafa nama sosai kamin a ci shi.

Kayan ganyaye, madara ko kayan nama, ya kamata a shirya su a sabonsu. Abincin da aka dafa a danyen sa yafi tsabta da dadi da kuma inganci. Yawancin kwayoyin cuta suna kara yawa a abincin dake ajiye, wanda ke da hatsari ga anta da kunhu.

Sanyaya abinci da ruwa bata tabatar da kiyayewa ba. Kwayoyin dake kawo cutar zawo kamar salmonella, da listeria zasu iya girma a cikin sanyayar abinci. Abincin da aka ajiye cikin na’urar sanyaya abinci, kada a ci shi sau da yawa ko kuma a dinga duma shi.

Abincin da aka dafa sai a rufe shi da kyau, idan za a dade kafin a ci. Abincin dake bude suna jawo kura da kudaje, wanda dukansu ke kawo cuta da kuma yada kwayar cuta.

Tsabta wajen rabon abinci shima yana da mahimmanci sosai. Mutanen da ke girki da kuma rarraba abinci ya kamata su tsabtace hannuwansu, su kuma yanke farce.

Kwanon raba abincin, chokali, sauran kwanuka da kuma sauran kayan amfani suna bukatar a tsabtace su, domin kwanuka marasa kyau zasu iya zama hanyar samu da yada kwayoyin cuta.

Chin abinci cikin kwano daya da amfani da kofi da gilasai domin shan ruwa, zai iya zama wata hanyar nuna kauna ne amma wata hanyar yada kwayar cuta ne.

Wanke hannuwa kamin cin abinci yana tabbata kiyayewar cututtuka da yawa.

Haka nan kuma yana da amfani cewa duk dattin da aka samu lokacin girki a jefa su cikin kwandon shara ko kuma rami da shirin kona su da wuta. Kada a kyale su su ruba domin wannan yana janyo cututtuka dake samuwa daga kudaje da sauran kwari.

Dokar gwamnati a wurin cin abinci na jama’a, hotel da sauransu, gameda tsabtar abinci suna da mahimmanci wajen kiyaye dafin abinci.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG