Mataimakiyar shugabar Amurka, Kamala Harris ta samu tarba daga 'yan makaranta da masu kade-kade da raye-raye na gargajiya, a lokacin da ta isa filin tashi da saukar jiragen sama na Kotoka na kasar Ghana.
A ziyararta ta mako guda zuwa nahiyar Afrika, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta isa kasar Ghana ranar Lahadi don tattaunawa kan batutuwa da yawa, ciki har da tattalin ariki.
Jami’an hukumar kula da shige da fice Kwastam na jamhuriyar Nijar sun fara yajin aikin kwanaki biyu da nufin nuna rashin nuna rashin jin dadinsu game da tsarin daukar sabbin ma’aikata na gwamnatin kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta fara bikin ne a shekarar 2013, kuma taken bikin wannan shekarar ta 2023 shi ne: “A yi La’akkari. A yi Godiya. A yi Kirki.
Wasu ‘yan ci rani ‘yan asalin kasashen yammacin Afrika da aka tuso keyarsu daga Libya, sun yi zaman dirshan a ranar Litinin a ofishin hukumar kula da kaurar al’umma IOM, dake birnin Yamai da nufin nuna kosawa da rashin mayar da su gida kamar yadda aka yi masu alkawali a baya.
Sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyarar wuni biyu a jamhuriyar Nijar ya sanar da karin kudaden tallafi ga kasashen yammaci da tsakiyar Afrika wadanda za'a yi amfani da su don inganta rayuwar al’umomin wadannan kasashe.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ziyarci Nijar tare da yin alkawarin ba da agaji ga mutanen da suka rasa matsugunansu da kuma tallafawa kokarin kasar na yaki da ta'addanci.
Matan kan gudanar da wannan aiki ne ko a wane irin hali na yanayi da ake ciki, kamar na rana ko ruwa ko sanyi.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Jamhuriyar Nijar a yau Alhamis 16 ga watan Maris inda zai tattauna da takwaransa Hassoumi Massaoudou ( Hasumi Masa’udu) kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu masu dadaddiyar huldar diflomasiya.
Rundunar da ke yaki da mayakan Boko Haram a kan iyakar Najeriya da Kamaru ta ce akalla mutane 3,000 ne suka rasa matsugunansu a wani sabon fadan mayakan Boko Haram da ya barke kwanan nan.
A wani mataki na tunkarar ta'addanci a yankin Tafkin Chadi ta dukkannin bangarori, rundunar kawancen yankin wato MNJTF ta matsa kaimi wajen afkawa ba kadai kan ‘yan ta'addan ba, har da karin samame akan fararen hular da ke taimakon ‘yan ta'addan wajen samar masu da kayayyaki ko bayanai.
Kasashen Malawi da Mozambik na kokarin ceto wadanda suka tsira daga mahaukaciyar guguwar Freddy a ranar Laraba yayin da adadin wadanda suka mutu ya haura 270 sakamakon guguwar mai karfi da ta afkawa yankin kudancin nahiyar Afirka.
Domin Kari