Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Zuba Jari A Yaki Da Ta'addanci A Yakin Sahel-Antony Blinken


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ziyarci Nijar tare da yin alkawarin ba da agaji ga mutanen da suka rasa matsugunansu da kuma tallafawa kokarin kasar na yaki da ta'addanci.

Mazauna babban birnin Yamai da Muryar Amurka ta zanta da su galibi suna da abubuwa masu kyau da suka fada game da ziyarar farko da sakataren harkokin wajen Amurka ya kai a kasar.

"Mun ga yadda a yau sojojin Amurka da ke yankin Nijar ke horar da jami'an tsaro da sojoji," wata mata a birnin Yamai tana shaida wa Sashen Faransancin Afrika na Muryar Amurka. Sai dai ta ce bai kamata a yi hadin gwiwa a fannin tsaro kawai ba.

“Akwai damammakin hadin gwiwa da dama a cikin shirin sauyin yanayi. Haka kuma akwai batun ruwa mai tsafta, akwai abubuwa da yawa,” inji ta.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar

Blinken ya yi amfani da wannan tafiya wajen sanar da tallafin dala miliyan 150 a cikin sabon taimakon jin kai don taimakawa wajen biyan bukatu a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka da kuma yankin Sahel da rashin zaman lafiya ya haifar.

Bayan taimakon gaggawa ga 'yan gudun hijira da sauran kungiyoyi masu rauni, Amurka ta kuduri aniyar saka hannun jari kan dorewar zaman lafiyar yankin, in ji Blinken.

Amurka za ta taimaka wajen karfafa hukumomin binciken manyan laifukan a Nijar domin yakar ta’addanci, da karfafa tsaron iyakoki, da inganta hanyoyin yaki da safarar miyagun kwayoyi, da dakile fataucin mutane, da kuma taimakawa wajen gudanar da bincike, gurfanar da su gaban doka, da kuma rage ta’addanci da tsattsauran ra’ayi,” in ji Blinken yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da takwaransa na Nijar a Yamai.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Na Ziyarar Aiki A Nijar

Amurka dai na da sojoji a sansanonin sojin sama guda biyu a kasar, kuma tana tallafawa sojojin Nijar da horo, da tallafin kayan aiki, da kuma taimakon leken asiri, sa ido da kuma bincike don yaki da ta'addanci.

Wani mazaunin Yamai da Muryar Amurka ta zanta da shi ya ce tallafin kayan aikin soji ya taimaka, amma ya bukaci shugabannin siyasa su yi taka tsantsan.

Kasar Nijar na kan gaba wajen fama da tashe-tashen hankula da fadace-fadace a yammacin Sahel, in ji Joseph Siegle daraktan bincike a cibiyar nazarin dabarun Afirka (ACSS). Kasar ta samu karuwar tashin hankali da kashi 43% a shekarar 2022, amma mace-macen ya ragu da rabi, in ji cibiyar ta ACSS.

Yayin da kasashen Burkina Faso da Mali da kuma Chadi suka fuskanci juyin mulki ko hargitsin siyasa, Nijar na ci gaba da gudanar da mulkin dimokradiyya.

XS
SM
MD
LG