Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta gudanar da wani taron tattaunawa kan karfafa tattalin arzikin mata a kasar Ghana, tare da jaddada kudirin gwamnatin kasar Amurka kan batun ci gaban mata a nahiyar Afirka baki daya, a ranar karshe ta ziyarar kwanaki uku da ta yi a kasar Ghana.