Air Marshall Moyo yace lalle suna bukatar taimakon sojin saman Najeriya wajen gyara jiragen yakinsu samfurin F7 da Mi35 wadanda Najeriya ita ma tanada irinsu kuma tana fafatawa dasu yakin da takeyi da yan ta’adda.
Bugu da kari, kasar ta Zimbabwe na neman Mayakan saman Najeriyar su tallafa mta a fannin fasahar Kurman jirgin nan maras matuki da kuma fannin bincike.
Babban Hafsan saman na Zimbabwe yace cikin lokaci kankani, Najeriya ta cimma gagarumar nasara wajen samarwa da kuma bunkasa fasaha a cikin gida a fannin jiragen yaki, abin ma kenan da yasa suka zo da kokon bara don neman agaji.
A jawabinsa, Babban Hafsan Hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Oladayo Amao ya bayyana cewa, a shirye suke su hada kai da Zimbabwen don a taimaka mata.
Air Marshall Amao yace bunkasa lamuran aiki tsakanin kasashen Afrika ka iya zama silar shawo kan kalubalen tsaro dake addabar nahiyar.
Amao yace hadin kai a fannonin horo da musayar fasaha zai karfafa karfin dogaro da kai tsakanin mayakan nahahiyar Afrika.
Hafsan mayakan na Zimbabwe a halin yanzu yana ziyaar aiki na tsawon mako guda a Najeriya, inda ake sa ran ya ziyarci rundunonin mayakan saman Najeriyar da kuma shiyyar Arewa maso gabashin Najeriyar.