Shugaban wata kungiyar asiri a Kenya ya shaida wa mabiyansa duniya za ta kare a ranar 15 ga watan Afrilu, ya umarce su da su kashe kansu da yunwa domin su kasance na farko cikin wadanda za su je aljanna, kamar yadda wani ‘dan uwan mabiyan kuma ma’aikacin asibiti ya shaida wa Reuters a ranar Laraba.
Gwamnatin Nijar ta ce ta samu nasarar kwashe jami’an diflomasiyyarta daga Sudan zuwa Djibouti a wani kokarin hadin gwiwa da kasar Faransa, sai dai wasu ‘yan kare hakkokin bil’adama na ganin ba a yi wa dalibai da sauran ‘yan Nijar mazauna Sudan adalci ba saboda yadda aka bar su a Khartoum.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada muhimmanci aiwatar da taron ƙolin ƙasashen yankin tekun Guinea wato "Gulf of Guinea Commission" mai fafutukar kare yankin daga ayyukan masu fashin teku.
Bangarorin da ke yaki da juna a Sudan sun amince da tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72 yayin da kasashen duniya ke yunƙurin fitar da 'yan ƙasarsu daga ƙasar.
Rikicin kasar Sudan ya saka direbobi da mamallakan motocin da ke jigilar kayayyakin kasuwaci daga jihar Diffa ta Jamhuriyyar Nijar zuwa kasar ta Sudan a cikin yanayi na zullumi.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta damu matuka da yadda rikicin kasar Sudan ke ci gaba a tsakanin Sojojin Kasar (SAF) da Dakarun ‘yan sa kai na (RSF), lamarin da ya janyo mace-mace da wahala ga fararen hula mara misaltuwa.
A jamhuriyar Nijar, direbobin motocin dakon itacen girke-girke sun bayyana damuwa dangane da abinda ka iya zama makomar wannan fanni da ke matsayin hanyar makamashin miliyoyin ‘yan kasar.
Masu ruwa da tsaki, ciki har da masana harkar tattalin arziki da tsaro sun bukaci kungiyar ECOWAS da tarayyar Afrika ta AU su dauki matakin shawo kan rikicin Burkina Faso da ke zama babbar barazana ga samar da abinci a wasu kasashen yammacin Afrika da yarjejeniyar kasuwanci ta AfCFTA.
Cibiyar kula da harkokin tattalin arziki ta bayyana damuwarta game da maimaita kura-kurai da gwamnatoci suka yi a baya wanda ya sanya tattalin arzikin Ghana ya tabarbare tsawon shekaru.
Shugabannin cocin katolika sun yi Allah wadai da yadda kisan gilla ke dada ta'azara a kasar, tare kuma da yin kira ga gwamnati ta kara tsaro da bincike, domin kare mutane da hukunta masu wannan aika aika.
Gwamnatin Najeriya tayi alkawarin bada goyon baya domin kaddamar da haddadiyar Kasuwar sufurin Afirka ta Sama (SAATM) Single African Air Transport Market. Lamarin da zai taimaka wajen bunkasa hada-hadar jiragen sama a Afirka.
Domin Kari