Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Ta Sa'o'i 72 Na Aiki A Sudan - Rahotanni


Sudan
Sudan

Bangarorin da ke yaki da juna a Sudan sun amince da tsagaita bude wuta ta sa'o'i 72 yayin da kasashen duniya ke yunƙurin fitar da 'yan ƙasarsu daga ƙasar.

Kuma rahotanni na nuni da cewa bangarorin biyu sun mutunta sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da suka cimma, sabanin wadanda suka gabata da suka yi fatali da su.

Rundunar Sojin Sudan (SAF) ta ce Amurka da Saudiyya ne suka shiga tsakani a tsagaita bude wutar, wanda ya fara daga karfe 12 na daren Litinin, agogon kasar.

Rikici tsakanin Dakarun Sojin Sudan da Dakarun sa kai (RSF) ya janyo asarar rayuka da dama tare da raba dubban mutane da muhallinsu.

A hira ta wayar taro da Muryar Amurka, Salman Al-Alfarisi, dan jarida a kasar Sudan ya ce, “Yau (Talata) an shiga rana ta biyu ba tare da mun ji ko da karar harsashi kwaya daya an harba shi sama ko karar bindiga, ko alamun za a dana bindiga za a harba”. Yace, ana hada-hada a kasuwanni dake gefen birnin Khartoum, domin an yi barna a cikin Khartoum sosai; an kona kasuwanni da manyan gidaje, domin haka sai sun fita kasuwannin bayan gari ko kauyuka suke samun yin siyayya.

Salman Al-Farisi ya kara da cewa, mazauna kauyuka sun fi ‘yan cikin Khartoum more rayuwa, da walwala domin, babu wutar lantarki, babu ruwan sha, kuma idan mutum ba shi da lafiya, asibitoci duka sun cika da wadanda suka jikkata.

Ya kara da cewa, wannan tsagaita wutar da aka yi, ta baiwa wadanda suke da aniyar ficewa daga kasar yin hakan.

Ko da yake, babu tashi da saukar jiragen sama domin sojin sa kai (RSF) sun kame filayen jiragen saman, amma dai mutane na amfani da motoci wurin ficewa ta iyakokin Masar, Habasha, Sudan ta Kudu, Chadi da Afirka ta Tsakiya.

A karshe Al-Farisi ya ce, babu wani alamun cewa wannan tsagaita wutar da aka yi zai sa bangarorin biyu da suke yaki da juna za su kai ga teburin tattaunawa domin, “suna kara kawo dakarunsu da muggan makamai a motoci, amma dai ba mu san abinda Allah zai yi ba”.

Akalla mutane 459 ne suka mutu, sai 4,072 suka jikkata sakamakon rikicin da aka shafe makonni ana gwabzawa a birnin Khartoum na kasar Sudan, a cewar wakilin hukumar lafiya ta duniya da ke Sudan.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG