Hankalin 'yan Najeriya ya koma kan sauran dalibai da su ka makale a kan iyakar Sudan da Masar bayan isowar rukunin farko na 'yan Najeriya 366 sun iso gida.
A shekara ta biyu jere, kasar Ghana ta sake faduwa a kididdigar ‘yancin ‘yan jarida ta shekara-shekara da kungiyar Reporters without Borders (RSF) ta fitar a ranar Laraba, ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya.
Ministan harkokin sadarwa na Jamhuriyar Nijar yayi jawabi game da matakan da gwamnati zata dauka domin kara bunkasa aikin jarida a Nijar, a daidai lokacin da shugaban hukumar kare hakkokin bil’adama na kasar yace 'yancin ‘yan jarida shi ne ke tabbatar da kafuwar dimokaradiyya a kasa.
Kungiyar karfafa ‘yan jarida mata a Afirka da ake kira Women In Journalism Africa ko WiJAfrica a takaice, ta fitar da sunayen mata 25 da suka yi fice da kuma gogewa a aikin jarida a shekarar 2023.
Hukumomin jamhuriyar Nijar sun kama shugaban kungiyar kare muradan jama’ar jihar Tilabery da shugaban wata jam’iyyar hamayya saboda zarginsu da furta kalaman da ke barazana ga zaman lafiya, sai dai wasu ‘yan fafutika na daukar matakin a matsayin bita da kullin siyasa.
Bayan kwashe su daga Sudan a ranar 25 ga watan Afirilun jiya an wuce kasar Habasha da su, daga nan kuma suka hau jirgin saman da ya karaso da su filin jirage na Kotoka da ke Accra a Ghana a ranar Talata 2 ga watan Mayun.
Wata tawagar daliban Najeriya da ke tserewa rikicin Sudan ta yi nasarar shiga kasar Masar kamar yadda ofishin jakadancin Najeriya ya tabbatar a ranar Talata.
Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa babu wani fasinja da ya samu rauni bayan aukuwar hadarin.
Masu Sharhi sun bayyana damuwa dangane da makomar bakin da suka makale a Sudan sakamakon yadda aka fara zargin wasu bakin da zama sojan hayar da ke kama wa bangaren ‘yan tawaye.
Wani binciken kasa da kasa ya bankado bayanan dake nuna alamun hannun tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou a badakalar da karkashinta ake zargin mahukuntan Nijer sun hada kai da kamfanin Areva don sayar da tonne 2500 na karfen uranium ta bayan fage a shekarar 2011.
Domin Kari