Kasar Habasha za ta hada kai da mahukuntan Saudiyya domin gudanar da bincike kan zargin da wata kungiyar kare hakkin bil'adama ta yi cewa, jami'an tsaron kan iyakar kasar sun kashe daruruwan bakin haure daga kasar, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar a ranar Talata.
Babban alkali mai shigar da kara a kotun daukaka kara ta birnin Yamai ya yi kashedi ga wasu wadanda ya ce suna yada labarai da kalaman da ke barazanar ta da fitina a wani lokacin da ake matukar bukatar ganin ‘yan Nijar sun kasance tsintsiya madaurinki daya.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan ayyukanta, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 26 ga watan Yuli, in ji wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.
Yayin da ECOWAS ta yanke shawara kan ranar da za ta aika dakarunta zuwa Nijar, bayan taron kwana biyu a birnin Accra, shugaban jam'iyyar adawa ta GUM, Rev. Christian Kwabena Andrews ya yi barazanar yin da zanga-zanga idan har Gwamnatin Ghana ta baiwa ECOWAS dakaru soja domin yaki a Nijar.
Shugabannin Musulmai, a karkashin jagorancin limamin limaman Ghana, Dakta Sheikh Usman Nuhu Sharubutu, sun yi kira da kada a dauki matakin soja wajen maido da mulkin dimokradiya a kasar Nijar, domin zai kawo asarar rayuka.
Wani harin ta’addancin da aka kai a kauyukan jihar Tilabery da ke Nijar ya yi sanadin rasuwar jami’an tsaro da dama a lokacin da suke kokarin kwato tarin shanu da maharan suka sace a karkarar Anzourou.
Somaliya ta bi sahun wasu kasashe wajen haramta TikTok, da kuma hanyar aika sakon Telegram da gidan yanar gizo na 1XBet domin dakile yada ayyukan batsa da lalata da wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma farfaganda, in ji ministan sadarwar kasar
Shugaban majalissar sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana fatan gudanar da al’amuran mulkin rikon kwaryar na tsawon wa’adin da bai kamata ya wuce shekaru uku ba.
Kakakin rundunar, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya shaidawa Muryar Amurka cewa irin wannan yunkuri ne da ya haddasa karancin kayayyakin bukatun yau da kullum ya sa 'yan ta'addan ke ta mika wuya ga dakaru.
Wannan tawagar ta je Jamhuriyar Nijar ne karo na biyu da nufin tantaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Daruruwan daliban Jamhuriyar Nijar da ke fatan shiga jami’oin Faransa sun fada halin zullumi sakamakon rashin samun takardar biza bayan da gwamnatin Faransar ta rufe ofishin jakadancinta a birnin Yamai sanadiyyar yanayin siyasar da aka shiga a kasar.
Domin Kari