Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Yi Watsi Da Shirin Sojojin Nijar Na Mika Mulki Bayan Shekaru Uku


Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO (Hoto: Facebook/CEDEAO/ECOWAS)
Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS/CEDEAO (Hoto: Facebook/CEDEAO/ECOWAS)

ABUJA, NIGERIA - Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO, ta yi fatali da shirin sojojin Nijar na mika mulki bayan shekaru uku.

Kwamishinan tsaro na ECOWAS Ambasada Dr. Abdel Fatah Moussa ya ce Jamhuriyar Nijar ta yi sabon Kundin Tsarin Mulki a shekarar 2010, inda aka sake yin bitarsa a shekarar 2017, kan wane irin gagarumin sauyi ake bukata a cikin shugabanci da za a bukaci kankame madafun iko har na shekaru uku.

Moussa ya kara da cewa, a wasu kasashen Afirka ta yamma da ke karkashin mulkin soja, sojojin sun yi shekaru ukun amma har yanzu suna hankoron neman karin watanni 18.

"Saboda haka wane hallaci sojojin Nijar ke da shi na son yin mulki har shekaru uku? Mun san kuma ba anan za a tsaya ba, saboda haka wannan lamari ba zai yi wu ba, saboda haka ECOWAS na son dole ne a sake maido da Nijar bisa tsarin doka, wannan shi ne matsayinmu." In ji Moussa.

A cewar Moussa, wannan mataki da sojojin suka dauka, "wannan takalar fada ne, tamkar suna fada mu yi duk abin d za mu yi ne."

Tun a baya dai masana a fannin kimiyyar siyasa irinsu Farfesa B.B. Faruk na Jami'ar Abuja suke ta cewa a yi hattara waje daukan matakin soji don shawo kan rikicin na Nijar.

"Ta ya ya za yi amfani da yaki a cimma wata nasara mai dorewa, bayan jama'ar da suke hade a wadannan wurare suna da shakka kan manufar da ake so a cimma."

Jihohin bakwai ne a arewacin Najeriya suke da iyaka da Jamhuriyar Nijar, wadanda duk kasance a kulle sakamakon takunkumin da ECOWAS ta kakabawa kasar.

Ya kara da cewa, "A karshe idan ECOWAS da take nuna dole sai ta yi amfani soja ta cimma wannan bukata, to ko da ta shiga da soja, sai da ta samu bukata daya, wato kasar Nijar ta farrasa, Najeriya ma ta farraka."

Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:

ECOWAS Ta Yi Watsi Da Shirin Sojojin Nijar Na Mika Mulki Bayan Shekaru Uku. mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG