WASHINGTON, D. C. - Kungiyar ta kuma sake yin kira ga jagororin juyin mulkin da su saki zababben Shugaban kasar Mohamed Bazoum, su kuma koma barikinsu.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU ya lura da matakin da kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta dauka na samar da rundunar da za ta taimaka wajen shiga tsakani na soji, sannan ta bukaci hukumar ta AU da ta tantance illar da ka iya samun tattalin arziki, zamantakewa da tsaro da ke tattare da tura irin wannan runduna.
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta ce a shirye take ta tura dakaru zuwa Nijar, idan yunkurin diflomasiyya na maido da dimokradiyya cikin kasar ya ci tura.
Har ila yau, kungiyar ta yi kira ga daukacin kasashe mambobinta da kasashen duniya da su kaurace wa duk wani mataki da zai iya halasta mulkin sojojin Nijar, ta kuma ce ta yi watsi da katsalandan daga wani ko wata kasa da ke wajen Afirka.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna