Matakin na zuwa ne sakamakon janye wasu ayyukan tallafawa 'yan cirani da kasashen suka yi bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.
Wani rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a karshen makon jiya ya ayyana cewa kungiyar IS ta yi nasarar ninka hare-haren da take kai a kasar Mali sau biyu a tsawon shekara cikin shekara guda, abin da ke fayyace girman mamayar da kasar ta Mali ke fuskanta daga kungiyoyin ta’addanci.
Jakadan Faransa a Nijar zai ci gaba da zama a kasar duk da matsin lambar da shugabannin da suka yi juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli ke nunawa, a cewar hukumomin Faransa.
Kakakin rundunar kawancen kasashen yankin tafkin Chadin MNJTF Laftanar kanar Abubakar Abdullahi ya yi bayanin cewa kwamandan sashi na biyu na rundunar, Manjo Janar Djouma Youssouf Mahammat Itno ne ya jagoranci mika ‘yan Boko Haram din ga hukumomin kasar.
Tarihi na nana cewa Hausawa ne suka kafa kusan duk zanguna da suke cikin Ghana. Domin haka ne harshen Hausa ya kasance harshen da ake mu’ammala da shi a matattarar al’ummu da ake cewa Zango a Ghana.
Hukumomin Nijar sun umarci jakadan Faransa Sylvain Itte da ya fice daga kasar a cikin sa'o'i 48 daga ranar Juma’a 25 ga watan Agusta, sai dai ma’aikatar harakokin wajen Faransa a na ta bangare ta yi watsi da matakin.
Gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar ta amince wa dakarun kasashen Mali da Burkina Faso su shiga kasar don bin sawun ‘yan ta’adda a duk lokacin da bukatar hakan ta taso a ci gaba da karfafa matakan yaki da kungiyoyin jihadin da suka addabi yankin Sahel.
Jamhuriyar Nijar ta bai wa sojojin Mali da Burkina Faso izinin shiga cikin kasarta idan har aka kai hari, a wata sanarwar hadin gwiwa da kasashen suka fitar a ranar Alhamis ta nuna.
A karo na biyu a cikin kasa da mako biyu, wata tawagar Malaman addinin Islama daga Najeriya ta kai ziyaraa jamhuriyar Nijar a yammacinranar Laraba, inda suka gana da Shugaban sojojin da suka yi juyin mulki Janar Abdourahaman Tchiani da Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine.
Kimanin ‘yan Afirka 7,000 da suka yi watsi da niyyar yin kaura zuwa Turai ne suka makale a Nijar tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan da ya gabata.
Wasu mutane goma sha biyu da suka tsallake rijiya da baya a yunkurin yin kaura ta hanyar teku zuwa Turai sun samu saduwa da iyalansu a Senegal, mako guda bayan an gano su a tekun Atlantika na kasar Cape Verde.
Kungiyar hadin kan kasashen Afrika ta dakatar da Nijar daga duk wasu aikace aikacen da suka shafe ta da cibiyoyin ta, har sai an maido da ingantacciyar Dokar Tsarin mulki, sakamakon juyin mulkin da ya faru a watan jiya.
Domin Kari