Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar MNJTF Ta Mika Wa Gwamnatin Kasar Tchadi Wasu Tubabbun ‘Yan Boko Haram Guda 46

'Rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Tchadi ta mikawa gwamnatin kasar Tchadi wasu tubabbun ‘yan Boko Haram guda 46

Kakakin rundunar kawancen kasashen yankin tafkin Chadin MNJTF Laftanar kanar Abubakar Abdullahi ya yi bayanin cewa kwamandan sashi na biyu na rundunar, Manjo Janar Djouma Youssouf Mahammat Itno ne ya jagoranci mika ‘yan Boko Haram din ga hukumomin kasar.

An dai mika su ne ga ministan kula da walwalar jama'a na kasar Chadi Hon. Abdoullaye Mbodou Mbam,i a garin Bagasola a wani bangare na irin hobbasa da rundunar MNJTF din da gwamnatocin shiyyar keyi na karfafa gwiwar yan ta'addan su ajiye makami.

'Rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Tchadi ta mikawa gwamnatin kasar Tchadi wasu tubabbun ‘yan Boko Haram guda 46
'Rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Tchadi ta mikawa gwamnatin kasar Tchadi wasu tubabbun ‘yan Boko Haram guda 46

Kwamandandan sashi na biyu na dakarun kawancen Manjo Janaral Itno ya nemi sauran mayakan Boko Haram din da ke cikin daji da su yi koyi da wadannan sama da arba'in din da su ka yi saranda.

'Rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Tchadi ta mikawa gwamnatin kasar Tchadi wasu tubabbun ‘yan Boko Haram guda 46
'Rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Tchadi ta mikawa gwamnatin kasar Tchadi wasu tubabbun ‘yan Boko Haram guda 46

Kwamandan kazalika ya kuma nemi sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al'umma da su ci gaba da taka rawa wajen yakar tsattsauran ra'ayi da ke zama makamashin ta'addanci a yankin.

A cewar wani masanin tsaro Farfesa Mohammed Tukur Baba lalle wannan mika wuya da yan ta'addan ke yi dayan biyu ne, imma ko don irin ruwan wuta da dakarun yankin ke masu ba kakkautawa ko kuma sun gaji da tada kayar baya da rayuwa cikin kunci a cikin daji.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG