Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Rikon Kwarya Ta Ce Bashi Ya Yi Wa Nijar Katutu A Zamanin Hambararriyar Gwamnati


Fira Ministan gwamnatin Rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine
Fira Ministan gwamnatin Rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine

Gwamnatin rikon kwaryar jamhuriyar Nijer ta bayyana cewa ta tarar da tarin bashin dubban billion cfa da hambararriyar gwamnatin kasar ta ci galibi daga kasashen waje.

To amma duk da haka ta yi nasarar biyan albashin watannin Yuli da Agustan da suka gabata ta hanyar kudaden da ta ce ta tattara daga harajin cikin gida duk da takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar a sanadiyyar juyin mulkin 26 ga watan Yuli.

Fira Ministan gwamnatin Rikon kwarya da ke bayani a taron manema labaran da ya kira ya fara da musanta kalaman da shugaba Macron na Faransa ya yi wa sojojin Nijer da yace sun kauracewa fagen daga don maida hankali akan maganar rike madafun iko. Ali Mahaman Lamine Zeine yace dakarun kasar sun kara jan damara a ci gaba da yaki da ta’addanci.

Ya kara da cewa gwamnatin rikon kwaryar ta tarar da billion ko kuma milliard 5200 na cfa na bashin da shudaddiyar gwamnatin Nijer ta ci daga cikinsu miliard 3200 daga kasashen waje abin da ke nufin bashi ya yi wa kasar katutu.

Sai dai duk da haka a cewarsa sun biya albashin ma’akata da jami’an tsaro na watannin Yuli da Agustan 2023 daga kudaden da suka samar a nan cikin gida daga lokacin da suka karbi madahun iko kawo karshen watan jiya.

A cewarsa sun dukufa wajen daukar matakan da za su taimaka daliban faramari da na sakandare da na jami’o'i komawa azuzuwansu a sabuwar shekarar karatun da ke shirin kamawa a watan gobe da dai sauarn bukatun al’umma.

Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce sun kaddamar da yunkurin ganin an cire wa Nijer dukkan takunkuman da kungiyar kasashen yammacin Afrika ta kakaba wa kasar.

Haka kuma ya jaddada cewa a shirye kasar ta ke ta maida martani ga dukkan wani yunkurin amfani da karfain soja kamar yadda ECOWAS ta yi barazana a baya.

Batun hukunta masu laifuka, wato masu cin hanci da mahandama, na cikin abubuwan da fira minista ya tabo a ganawarsa ta farko da manema labarai.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG