Iran ta fada jiya Laraba cewa, a shirye take ta taimaka wa Jamhuriyar Nijar da aka yi juyin mulki, don shawo kan takunkumin da kasashen duniya suka kakaba mata, a daidai lokacin da Tehran ke kokarin rage maida da ita saniyar ware da aka yi, ta hanyar karfafa alaka da kasashen Afirka.