Alhaji Banda, yace duk da karin kudade da aka samu na gudanar da aikin Hajji a kasar Saudiyya a bana, hukumar alhazan Ghana, bayan ta yi nazari sosai, tace za ta cika alkawarin da ta dauka na kin karin kudin hajjin bana.
Alhaji Banda yace, har yanzu kudin hajjin bana bai sauya ba, maniyyata za su biya GHC 75,000, wanda ya yi daidai da dalar amurka $6,250.
"Mun yi alkawari cewa, idan darajar dala ($) ta hau, kuma darajar sidi (GHC) ta sauko, ba za mu kara kudin hajjin wannan shekarar ba. Don mu cika alkawarinmu, kudin hajji na wannan shekarar shi ne GHC 75,000. Don haka duk wanda yake da niyyar zuwa hajji wannan shekarar sai su fara biya yanzu ga ajentocin hukumar alhazai, ko a biya kai tsaye ga hukumar, ko kan manhajar da hukumar ta bude domin biyan kudin hajji daga ko’ina", in ji shi.
Alhaji Banda ya kara da cewa, kudin na kunshe ne da farashin biza, kudin jirgi daga Ghana zuwa Saudiyya da dawowa; da sufuri daga Madina zuwa Makkah, Makkah zuwa Mashaa'ir, Mina, da Arafat, da Mashaa'ir zuwa filin jirgin saman Jiddah, da kudin otel, da ciyarwa a can na wata daya da sauransu. Yace, za a rufe amsar kudaden maniyyata daga ranar 15 ga watar Maris 2024.
Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Farouk Hamza, ya yi kira ga maniyyata da kada su biya kudadensu ga wasu ajentocin da hukumar ba ta amince da su ba.
"Kowa ya san bizan shekara daya daban ne da bizan hajji. A nan Ghana, hukumar alhazai ce kadai gwamnatin Ghana da na Saudiyya suka amince da su gudanar da aikin zuwa hajji. Don haka, duk wanda yake da niyyar zuwa hajji, bai yiwuwa sai da hannun hukumar alhazai na Ghana", a cewarsa.
Shugaban Ajentocin Hajji na Ghana, Alhaji Alhassan ya jaddada muhimmancin kin biyan kudade ga ajen da hukumar ba ta aminta da su ba. Yace, shekarar da ta gabata sun bayyana matakin da za su bi wajen dakile hakan, wanda ya yi sanadiyar rashin nasara, amma wannan shekarar ba za su bayyana ba.
Ya kara da cewa amma sun shirya tare da hukumar Saudiyya matakan da za su dauka na hukunta duk wanda aka kama.
Hukumar tace kamar shekarar da ta gabata, otel din Ghana na kusa da masallaci ne a Madina, kuma a Makka, akwai bas-bas da za su yi jigilar alhazai zuwa harami kyauta.
A saurari cikakken rahoton Idris Abdullah:
Dandalin Mu Tattauna