Wani jami'in shari'ar kasar Tunisia ya sanar a ranar Alhamis cewa an gano gawarwakin 'yan ci-rani 13 'yan kasar Sudan, yayin da wasu 27 suka bace bayan wani jirgin ruwa ya nutse a ranar Laraba a gabar tekun Tunisiya bayan da ya taso daga Sfax.
Kasar Mali ta fada a ranar Laraba cewa, ba za ta jira shekara guda kafin ta fice daga kungiyar ECOWAS ba, kamar yadda yarjejeniyar kungiyar ta bukata.
A ranar Talata ne majalisar ministocin zartarwar kasar Zimbabwe ta amince da soke hukuncin kisa bayan shafe tsawon watanni ana muhawara a majalisar dokokin kasar, inda a maimakon haka ta zabi yanke hukuncin daurin shekaru a gidan yari bisa munanan laifuka.
Hukumomin Kiwon Lafiya a Nijar sun tabbatar da bullar cutar mashako ko diphtheria a Arewacin kasar inda tuni mutane 70 suka kamu da cutar yayinda bakwai suka rasa rayukarsu.
Kasashen biyu dama sun dade da jure hamayya ta tsawon shekara guda, saboda su ne ke da masana'antun nishaɗi mafiya girma a Afirka, kuma kusan su ne mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar.
Bayan da a ranar Litinin 'yan majalisar dokokin Senegal suka kada kuri'ar dage zaben shugaban kasa na ranar 15 ga watan Disamba, sakamakon zanga-zangar da al'ummar kasar suka yi, lamarin ya sa wasu 'yan majalisar adawa suka hana gudanar da kada kuri’ar har sai da jami'an tsaro suka shiga tsakani.
A yau Talata ne aka gurfanar da shugaban kungiyar asiri na kasar Kenya Paul Mackenzie tare da wasu mukarrabansa 29 da laifin kisan yara 191 da aka gano gawarwakinsu sama da ninki biyu na adadin da aka binne a wani daji.
Kasar Jamhuriyar Nijar ta cimma wasu yarjeniyoyi da dama a tsakanin ta da kasashen Turkiya da Iran ta bangaren tattalin arziki, tsaro, noma, gine ginen gidaje da hanyoyi da dai saurensu.
Matakin dage zaben da Shugaba Macky Sall na Senegal ya sanar a jawabin da ya yi wa al’ummar kasar ta kafar tabijan a ranar asabar din da ta gabata a jajibirin ranar kaddamar da yakin neman zabe ya dauki hankulan masana harakokin siyasa da dimokradiyar kasashen Afrika.
Kwana daya kafin a soma yakin neman zaben shugaban kasa a Senegal, shugaba Macky Sall ya sanar da dage zaben kasar saboda rikicin da ke faruwa tsakanin majalisar dokokin kasar da kotun tsarin mulki, a cewarsa.
Akalla mutane 39 suka mutu a fada da ta barke tsakanin makiyaya daga jihohi biyu da ke makwabtaka a Sudan ta Kudu,in ji jami'ai, inda suka dora alhakin rikicin kan filaye da aka dade ana yi.
Hukumomin kasar Maroko sun kama mutanen 30 a wannan makon a birnin Fes bisa zargin safarar jarirai.
Domin Kari