Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar Ta Cimma Sabbobin Yarjeniyoyin Hulda Da Kasashen Iran Da Turkiya


Firai Minstan Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine a Turkiya tare da Shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan
Firai Minstan Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine a Turkiya tare da Shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan

Kasar Jamhuriyar Nijar ta cimma wasu yarjeniyoyi da dama a tsakanin ta da kasashen Turkiya da Iran ta bangaren tattalin arziki, tsaro, noma, gine ginen gidaje da hanyoyi da dai saurensu.

AGADEZ, NIGER - Bangarorin sun cimma wannan matsaya ce a ziyarar aiki da Shugaban gwamnatin, Nijar Lamine Zein, ya kai a kasashen a wani mataki na neman mafita ga takunkumin tattalin arziki da ECOWAS da kuma wasu kasashen duniya suka sanyawa kasar.

Firai Minstan Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine
Firai Minstan Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine

A yayin wata ziyara da Firai Ministan na Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine ya kai a kasashen na Iran da Turkiya ne suka kulla yarjejeniyar tsaro da kara inganta hulda ta fannonin ci gaba da dama a tsakanin kasashen.

Tawagar Firai Ministan dai ta kunshi Ministoci shida da suka hada da na tsaro da man fetir da na noma da kuma kasuwanci.

Firai Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine lokacin da ya kai ziyara Iran
Firai Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine lokacin da ya kai ziyara Iran

Makasudin wannan ziyarar dai ita ce kokarin samar wa kasar Nijar mafita daga takunkuman kasashen Africa ta yamma da ECOWAS wanda suka kakaba mata, matakin da yakai ga kulla yarjejeniyar kasuwanci da wadannan kasashen a cewar Firai Ministan Nijar, Ali Lamine Zaine.

Masana irin su Alkassoum Mato na ganin akwai bukatar Nijar ta inganta huldarta da sabbin kasashe irin su Tukiya da Iran.

Firai Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine da shugabn kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan
Firai Ministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zaine da shugabn kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan

Yanzu dai ‘yan kasar Nijar sun zura ido su ga sakamakon wannan yarjejeniya daga gwamnatin wadannan kasashe wajen taimakawa Nijar fita daga cikin matsalolin da take fuskanta sakamakon takunkuman tattalin arziki da kasashen Afirka ta yamma suka saka mata bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar da ta gabata, tun daga bayan juyin mulki da kuma raba gari da kasar Faransa.

Al’umma a Nijar da dama sun bayyana fatan ganin kasar su ta karfafa huldarta da kasashen Rasha da turkiya da kuma Iran, musamman a fannin tsaro.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Jamhuriyar Nijar Ta Bullo Da Sabon Babin Hulda Da Kasashen Iran Da Turkiya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG