WASHINGTON, D. C. - Wadanda ake tuhumar dai duk sun musanta laifin da aka shigar kara gaban wata kotu a garin Malindi da ke gabar teku. An samu daya daga cikin wadanda ake zargi da rashin lafiyar tabbin hankali, da ba za a iya masa shari’a.
Masu gabatar da kara sun ce Mackenzie ya umurci mabiyansa da su kashe kansu ne da 'ya'yansu da yunwa domin su je lahira kafin karshen duniya, wanda yake daya daga cikin bala'o'i mafi muni da ke da alaka da kungiyoyin asiri a tarihin baya-bayan nan.
Mabiyan Cocinsa na Good News International sun zauna ne a wasu ƙauyuka da dama a cikin wani yanki mai girman eka 800 a cikin dajin Shakahola. Daga karshe dai an tono gawarwaki sama da 400.
An kama Mackenzie a watan Afrilun shekarar da ta gabata ne. Tuni dai aka tuhume shi da laifukan ta'addanci, kisa da azabtarwa.
Aka kuma yanke masa hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari a watan Disamba da laifin shirya fina-finai da rarrabawa ba tare da lasisi ba.
Mackenzie, wanda tsohon direban tasi ne, ya hana ‘yan kungiyar tura ‘ya’yansu makaranta da kuma zuwa asibiti a lokacin da suke rashin lafiya, yana mai cewa irin wadannan cibiyoyin na mabiya shaidan ne, in ji wasu mabiyansa.
Lauyan Mackenzie ya ce yana bayar da hadin kai wajen gudanar da bincike kan wadanda suka mutu. Alkalin ya ce mutane 30 da ake tuhumar za su dawo kotu ranar 7 ga watan Maris domin sauraren karar.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna