Sanarwar ta kara da cewar, an daina jin duriyar jirgin saman mallakin Ma’aikatar Tsaron Malawi bayan daya bar babbar birnin kasar, lilonge, a yau Litinin da safe.
Dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai hari babban asibitin da ke birnin Al-Fashir na Sudan kuma an dakatar da ayyuka a asibitin, abin da kungiyar likitocin agaji ta Doctors Without Borders (MSF) wacce ke tallafa wa asibitin ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters kenan a ranar Lahadi
An yi bikin kaddamar da ayyukan kwashe sojojin Amurka a hukumance da yammacin ranar Jumma’a a filin jirgin sojan sama da ke birnin Yamai na Jamhiriyyar Nijar.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya yi alkawarin karin goyon baya ga kasar Burkina Faso wajen yakar kungiyoyin 'yan ta'adda a yayin wata ziyara da ya kai yammacin Afirka a wani yunkuri na cike gibin da kawayen kasashen yammacin Turai suka bari yankin.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya bayar da rahoton cewa, a ranar 24 ga watan Mayu ne hukumar ICRC ta fara rabon abinci ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Kanyabayonga, amma bayan kwanaki shida suka dakatar da su.
Wani dan kasar Afrika ta Kudu ya bayyana a gaban kotu a yau Talata bisa zargin daba wa wata mace wuka har lahira tare da raunata mijinta da danta saboda ra’ayinsu na goyon bayan Falasdinu.
Kasar Amurka ta sanar da ware karin miliyoyin dala domin tallafa wa al’umomin da ke bukatar agaji a kasashen yammacin Afrika.
Bankin Duniya ya amince da baiwa Ghana bashin dala miliyan 250 don tallafawa harkokin hada-hadar kudi a wani aikin saisaita sashen kudin kasar na tsawon shekaru biyar, kamar yadda wata sanarwa da bankin Duniyar ya fitar.
Jam’iyyar wadda Nelson Mandela ya taba jagoranta ta lashe kujeru 159 ne kacal a cikin 400 inda a baya ta samu kujeru 230.
Wata tawwagar mataimakin ministan tsaron kasar Rasha hade da ta ‘yan kasuwar Rashar sun kai ziyara a jamhuriyar Nijar inda suka gana da hukumomin mulkin sojan kasar a ci gaba da karfafa hulda a sabon kawancen da kasashen 2 suka kulla a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Ana sa ran fitar da cikakken sakamakon zaben a karshen makon nan da mu ke bankwana da shi.
Mazauna Rafah sun ba da rahoton mummunar luguden wuta da harbin bindiga a yau Alhamis a birnin Gaza mai nisa da ke kudu bayan da Isra'ila ta ce ta kwace wata hanya mai mahimmanci a kan iyakar Falasdinawa da Masar.
Domin Kari