Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Sama Dauke Da Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Yayi Batan Dabo


Saulos Chilima, Mataimakin Shugaban Kasar Malawi
Saulos Chilima, Mataimakin Shugaban Kasar Malawi

Sanarwar ta kara da cewar, an daina jin duriyar jirgin saman mallakin Ma’aikatar Tsaron Malawi bayan daya bar babbar birnin kasar, lilonge, a yau Litinin da safe.

Wani jirgin sama dauke da Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Saulos Chilima da wasu mutane 9 yayi batan dabo.

Sakataren Shugaban Kasar shugaban kasar, Colleen Zamba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewar, an daina jin duriyar jirgin saman mallakin Ma’aikatar Tsaron Malawi bayan daya bar babbar birnin kasar, lilonge, a yau Litinin da safe.

Shugaban kasar ya bada umarnin gudanar da aikin ceto bayan da jami’an sufurin jiragen sama suka gaza jin duriyar jirgin.

Kamata yayi jirgin ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Mzuzu, dake shiyar arewacin kasar da misalin karfe 10 na safe agogon kasar.

Bayan da aka sanarda shi game da afkuwar lamarin, nan take shugaban kasar Lazarus Chakwera ya soke tafiyar da shirya yi zuwa tsibirin bahamas ta jirgin sama.

A cewar sanarwar, “ofishin shugaban kasa da majalisar ministoci na sanarda al’umma cewar jirgin sama mallakin Ma’aikatar Tsaron Malawi daya bar birnin Lilonge a yau Litinin, 10 ga watan Yunin da muke ciki da misalin 9 da minti 17 na safe, dauke da mataimakin shugaban kasa, rt honourable Klaus Chilima, da wasu mutum 9, ya gaza sauka a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Mzuzu da misalin karfe 10 na safiya kamar yadda aka tsara”.

“Za’a sanarda al’umma game da duk wani cigaba da aka samu akan lamarin da zarar an tabbatar da shi, a cewarsa

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG