Shugabanin gwamnatocin mulkin sojan Burkina Faso, Mali da Nijar na shirin gudanar da taronsu na farko a karkashin inuwar kungiyar AES a ranar Asabar 6 ga watan Yuli a birnin Yamai.
Wata kungiya dauke da makamai ta kai hari a yayin wani bikin aure a tsakiyar kasar Mali tare da kashe akalla mutane 21, kamar yadda mazauna yankin suka fada a ranar Laraba.
Shugaba Ruto dai na fuskantar rikici mafi muni tun bayan da ya kama aiki a shekarar 2022, inda wasu masu zanga zangar ke kiran ya sauka daga shugabancin kasan, suna mai zargin shi da rashin iya mulki.
Sabon Rahoton Ci Gaban Bil Adama na Ghana na 2023, wanda hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya , da hadin gwuiwar Hukumar Kididdiga ta Ghana da Hukumar Tsare-tsare ta Kasa suka fitar, ya bayyana cewa, rashin aikin yi ga matasa yana da matukar tayar da hankali.
Wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya ya ce yunwa a Sudan da yaki ya daidaita na cikin wani yanayi da ba a taba ganin irinsa ba, inda sama da mutane miliyan 25 ke fama da matsalar yunwa, wasu kuma 755,000 na cikin mawuyacin hali, da kuma hadarin fadawa yunwa a yankuna da dama.
'Yan sandan Kenya sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga da dama tare da toshe titunan hanyar zuwa fadar shugaban kasar a ranar Alhamis, yayin da ake ci gaba da gudanar da kananan zanga-zanga a garuruwa da dama.
Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makokin kwanaki uku daga yau Laraba bayan rasuwar sojojinta 20 da farar hula 1 lokacin wani harin ta’addanci da ya rutsa da su a kauyen Tassia na yankin Tilabery a jiya Talata.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta samu wani shugaban masu tsattsauran ra'ayin Islama mai alaka da al-Qaida da laifin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Timbuktu na kasar Mali.
Wata tawagar tsofaffin shugabanin kasar Benin ta kai ziyara Nijar domin tattaunar yiwuwar samar da maslaha a rikicin diflomasiyar da ya barke a tsakanin hukumomin mulkin sojan Nijar da gwamnatin jamhuriyar Benin sakamakon dambarwar da ta biyo bayan kifar da gwamnatin dimokradiya a watan Yulin 2023
Domin Kari