Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun ICC Ta Samu Shugaban Al-Qaeda Da Laifin Ta'addanci A Mali


Al Hassan Ag Abdoul Aziz Ag Mohamed Ag Mahmoud, shugaban ‘yan ta’adda masu alaka da Al-Qaida na Mali
Al Hassan Ag Abdoul Aziz Ag Mohamed Ag Mahmoud, shugaban ‘yan ta’adda masu alaka da Al-Qaida na Mali

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta samu wani shugaban masu tsattsauran ra'ayin Islama mai alaka da al-Qaida da laifin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Timbuktu na kasar Mali.

An zargi Al Hassan Ag Abdoul Aziz Ag Mohammed Ag Mahmoud da taka muhimmiyar rawa a mulkin ta'addanci da 'yan tada kayar baya suka kaddamar a birnin Hamada mai tarihi a arewacin Mali a shekara ta 2012

An zarge shi ne da hannu a laifukan da suka hada da fyade, azabtarwa, tsanantarwa da auren dole. Masu gabatar da kara sun ce shi mamba ne na kungiyar Ansar Dine mai tsatsauran ra'ayin Islama dake da alaka da al-Qaida dake rike da iko a arewacin Mali a lokacin.

Al Hassan na fuskantar hukuncin daurin rai da rai idan har aka yanke masa hukunci nan gaba kadan.

Masu gabatar da kara sun ce shi mamba ne na kungiyar Ansar Dine mai tsatsauran ra'ayin Islama da ke da alaka da al-Qaida da ke rike da iko a arewacin Mali a lokacin.

Mata da 'ya’ya mata sun sha wahala musamman a karkashin mulkin danniya na Ansar Dine, inda suke fuskantar hukuncin kisa da dauri, babbar mai shigar da kara ta kotun Fatou Bensouda ta bayyana a farkon shari'ar Al Hassan kusan shekaru hudu da suka gabata.

Bensouda ta ce "An tilasta wa mata da yawa yin aure. "An tsare su ba tare da son ran su ba, kuma 'yan kungiyar sun yi ta yi musu fyade." Ta kuma kara da cewa Al Hassan na da hannu wajen shirya irin wadannan aure, kamar yadda mai gabatar da kara ta shaida wa alkalai.

Ta ambaci wata da aka yi wa fyade tana cewa, “Abin da ya rage a ni gawa ce.”

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG