Haka shine lamarin da ya yi sanadin rufe iyakokin kasashen biyu da kuma dakatar da ayyukan bututun da Nijar ke amfani da shi wajen fitar da manta zuwa kasuwannin duniya a karkashin wata yarjejeniyar da ta hada da China da Benin da Nijar din.
Ganin yadda rikici ke kara kamari a tsakanin hukumomin mulkin sojan Nijar da hukumomin makwabciyar kasa jamhuriyar Benin ya sa tsofaffin shugabanin kasar Benin, Nicephore Dieudonné Soglo da Thomas Yayi Boni, fara ziyara a Nijar da nufin tuntubar hukumomin kasar ta yadda za su zaunar da bangarorin biyu su fuskanci juna domin warware wannan rikici da ya yi sanadin rufe iyaka a tsakanin kasashen biyu.
Tuni dai tawagar ta yi ganawar farko da ministan cikin gida Janar Mohamed Toumba a jerin zaman da zai hada su da mukarraban gwamnatin mulkin sojan Nijar, kuma ana sa ran yiwuwar ganawarsu a nan gaba da shugaban majalissar CNSP Janar Tiani a fadarsa. Abin da wani masanin huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye ke alakanta shi da tasirin diflomasiya a yunkurin warware kowace irin takaddama.
A baya hukumomin Nijar sun yi watsi da tayin sulhun da Benin ta zo da shi, inda Janar Abdourahamane Tiani ya ki ganawa da ministan da Patrice Talon ya turo dauke da wasikar biko a watan Mayun da ya gabata.
Amma masana na jan hankula a game da girman mu’amular kasashe a bisa tsarin tafiyar siyasar duniya.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna