Shugabanin al’ummar kabilar tubawa na jamhuriyar Nijar sun kudiri aniyar taimaka wa hukumomi domin tabbatar da tsaro a yankunan kasar da ke makwaftaka da Chadi.
Majalisar dokokin kasar Kamaru ta amince da kudurin dokar kara wa'adin 'yan majalisa da kansiloli kamar yadda shugaban kasar Paul Biya ya umurce su. Lamarin da a ya kawo cecekuce tsakanin jam’iyun adawa da suke ganin dabara ce ta hana su tsayawa takarar zaben shugaban kasa shekara mai zuwa.
Wata kotu a Nijar ta bada belin wani ‘dan jarida bayan da ya shafe watanni kusan uku a gidan yari saboda zargin yi wa sha’anin tsaron kasa karan tsaye.
Gwamanatin mulkin sojin Nijar ta soke lasisin kamfanin kasar Kanada na GOVIEX dake gudanar da wani aikin habbaka hakar uranium a arewacin kasar.
A yau Talata, Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya akan kare hakkin bil adama ya bayyana cewar ofishinsa na bibiyar rahotanni game da wani makeken kabari a rairayin Sahara dake kan iyakar kasashen Libya da Tunisiya bayan da a farkon shekarar nan aka gano gawarwakin bakin haure 65 a wani wuri daban
Sanarwar ta Jamus dai na zuwa ne a wani lokaci da kasar ta Nijar ta kawo karshen yarjejeniya da wasu kasashen yammacin duniya irin su Amurka da Faransa.
‘Yan Nijar sun fara mai da martani bayan da kungiyar CEDEAO ta jaddada aniyar ci gaba da tuntubar kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar don ganin sun sake komawa sahun mambobinta.
Sojojin Amurka sun kammala janyewa daga sansaninsu da ke Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar, kuma za su fice gaba daya daga kasar ta Agadez kafin cikar wa'adin ranar 15 ga watan Satumba da shugabannin sojan kasar suka sanya, a cewar kasashen biyu ranar Lahadi.
Hukumomin sojan Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi bikin raba gari da sauran kasashen yammacin Afirka a ranar Asabar, yayin da suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kafa wata kungiya a tsakaninsu.
Afirka ta Yamma mai rarrabuwan kai ta gudanar da tarukan kolin shugabannin kasa guda biyu a kasashe daban-daban biyu a karshen makon, inda aka gudanar da taro farko yau Asabar a Nijar tsakanin shugabannin mulkin soja na yankin Sahel.
A ranar Lahadi ne Amurka za ta kammala janye dakarunta da kayan aikinta daga sansanin sojin sama da ke Yamai babban birnin kasar Nijar a yammacin Afirka, tare da gudanar da bikin janyewar.
Domin Kari