Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Nijar Da Mali Da Burkina Faso Sun Kafa Kungiyar Hadaka


Shugabannin Nijar da Burkan Faso.
Shugabannin Nijar da Burkan Faso.

Hukumomin sojan Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi bikin raba gari da sauran kasashen yammacin Afirka a ranar Asabar, yayin da suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kafa wata kungiya a tsakaninsu.

Taron farko na kasashen uku, wadanda dukkaninsu suka fice daga kungiyar ECOWAS a farkon wannan shekarar, an kuma bukaci a kara yin hadin gwiwa a bangarori da dama.

“Mutanenmu sun juya baya ga kungiyar ECOWAS ba tare da wata tangarda ba,” in ji Janar Abdourahamane Tiani mai mulkin Jamhuriyar Nijar, ya shaidawa 'yan uwansa masu fada a ji a yankin Sahel a wajen bude taron da aka yi a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.

Shugabannin ukun da suka karbi mulki ta hanyar juyin mulki a shekarun baya-bayan nan, sun yanke shawarar daukar wani mataki na kara samun hadin kai, tare da amincewa da yarjejeniyar kafa kungiyar, a wata sanarwa da suka fitar a karshen taron.

Kungiyar kasashen yankin Sahel da za ta yi amfani da sunan AES kuma za ta kasance karkashin jagorancin kasar Mali a shekara ta farko, adadin ya kai kimanin mutane miliyan 72.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG